Kyakkyawar Hulda Tsakanin Sin Da Amurka Za Ta Samar Da Kyakkyawar Makoma Ga Yanayin Duniya

[ad_1]


An yi tattaunawa ta wayar tarho a jiya Litinin da dare tsakanin shugaban kasar Sin Xi Jinping da takwaransa na Amurka Donald Trump, inda shugaba Xi ya bukaci bangarorin biyu su ci gaba da inganta daukaka tagomashin da dangantakarsu ta samu, ta yadda za su ci gaba da bin turbar da ta dace.

Duniya ta shiga wani yanayi na hargitsi da yake-yake a baya-bayan nan, lamarin da ya haifar da rashin tabbas da rashin kwanciyar hankali game da makomarta. A daidai wannan lokaci da ake ciki, abun da ake bukata shi ne hadin gwiwa da goyon bayan juna da watsi da bangaranci, domin ceto duniya da al’ummarta daga fadawa cikin mummunan yanayi fiye da wanda ake ciki, kuma domin tabbatar da hakan, ana matukar bukatar hadin gwiwar kasashe mafiya karfin tattalin arziki a duniya wato Sin da Amurka.

Har kullum kiran kasar Sin shi ne, mutunta juna da tabbatar da daidaito a tsarin huldar kasa da kasa da hada hannu domin samun moriyar juna da ci gaba na bai daya. Ya kamata yanayin da duniya ta fada, ya sa Amurka fahimtar cewa, ya kamata ta ajiye girman kai da ra’ayin mulkin danniya ko babakere, domin ba hakan duniya ke bukata. Yanzu ana wani zamani da ake samun karuwar karfi tsakanin kasashe da kara fahimtar cewa, suna da damar samun ci gaba ba tare da dogaro da tsarin wata kasa ba. Don haka, kamata ya yi Amurka ta rungumi abun da sabon zamani ya zo da shi, wato watsi da babakere, a yi hadin gwiwa don samun moriyar juna.

Hakika tattaunawar da aka yi jiya, wadda ta biyo ganawar da aka yi a baya-bayan nan a Busan na Koriya ta Kudu, kyakkyawan sako ne ga duniya wanda ke nuna cewa, har kullum, tattaunawa da yarjejeniya ita ce hanya mafi dacewa maimakon tankiya da fito na fito. Haka kuma sako ne da zai taimaka wajen ba kasashen duniya kwarin gwiwar cewa, akwai kyakkyawar makoma a gaba ta raya dangantakar Sin da Amurka da kuma inganta huldar kasa da kasa wadda ita ce kasashen duniya musammam masu tasowa suke da burin gani. Ko sanarwar taron G20 da aka kammala a ranar Lahadi, ta nanata muhimmancin hadin gwiwa da cudanyar kasa da kasa a matsayin mai muhimmanci wajen shawo kan kalubalen duniya, kuma idan har aka samu hakan karkashin kyakkyawar huldar da jagorancin Sin da Amurka, tabbas za a kai ga samar da duniya mai kyakkywar makoma ga daukacin dan adam. (Fa’iza Mustapha)

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *