Gwamnatin Kebbi Ta Bayar Da Umarnin Rufe Duk Makarantun Sakandare Da Jami’o’in Jihar

[ad_1]


Gwamnatin Jihar Kebbi ta umarci a rufe dukkanin makarantu da jami’o’in gwamnatin jihar nan take.

Wannan umarni ya fito ne daga Ma’aikatar Ilimi ta Jihar Kebbi.

Umarnin na cikin wata wasiƙa daga Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Abdullahi Fodio, Aliero.

Wasiƙar, wacce Sakataren Jami’ar, Maimaro Alhaji Tilli, ya sanya wa hannu, ta ce duk ma’aikata da ɗalibai dole su bar jami’ar nan take.

An umurci ɗalibai, daga manyan makarantu masu karantun digiri, difloma, IJMB, da sauransu da su fice daga harabar jami’ar cikin sa’a ɗaya.

Wasiƙar ta yi gargaɗin cewa jami’an tsaro za su kori duk wani ɗalibi da aka same shi a cikin ɗakunan kwana ko sauran wuraren jami’ar.

Haka kuma, ɗaliban da ke zaune a wajen jami’ar, kamar Gidan Rami da wasu wurare, an umarce su da su bar wuraren nan take don kaucewa matsala daga jami’an tsaro.

Kwalejin Ilimi ta Adamu Augie da ke Argungu ta fitar da irin wannan sanarwa, wacce ta umarci kowa da ya fice daga makarantar nan take.

Wannan mataki ya shafi dukkanin jami’o’i da kwalejojin da ke Jihar Kebbi.

A ranar Juma’a, Gwamnatin jihar ta kuma umarci a rufe dukkanin makarantun kwana a jihar.

Sanarwar ba ta bayyana dalilin rufe makarantun ba, kuma har yanzu jami’an gwamnati ba su bayyana tsawon lokacin da za su shafe a rufe ba.

Wannan dai na zuwa ne biyo bayan sace ɗalibai 25 a garin Maga da ke jihar.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *