Ɗalibai 215 da malamai 12 aka sace a Makaranta a Neja — CAN

[ad_1]



Yawan ɗaliban da aka sace a makarantar Sakandaren St. Mary’s da ke Jihar Neja ya kai 215 da kuma ma’aikata 12 a cewar Ƙungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN).

Shugaban Ƙungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN) Reshen Jihar Neja, Rabaran Bulus Dauwa Yohanna, ya ce mutum 227 aka sace a makarantar, ɗalibai 215 da kuma malamai 15.

A safiyar Juma’a ne ’yan bindiga suka kutsa makarantar da ke yankin Papiri da ke Karamar Hukumar Agwara ta jihar Neja suka yi awon gaba da su.

Da yake jawabi bayan ziyartar makarantar, ya bayyana cewa, “Na gana da iyayen ɗaliban kuma mun tabbatar musu cewa muna aiki tare da gwamnati da jami’an tsaro domin ganin an ceto yaran.

“Alƙaluman da aka tattara sun nuna yara 215 da malamai 12 ne ’yan bindiga suka yi garkuwa da su a garin.

“Akwai yaran da suka tsere a lokacin da aka kai harin, kuma iyayen sun zo suka kwashe ’ya’yansu tunda an rufe makarantu,” in ji shi.

Aminiya ba ta iya tabbatar da alƙaluman ba, kuma hukumomi ba su fitar da nasu alƙaluman ba, zuwa lokacin da muka kammala wannan labari.

Wakilinmu ya gano cewa da misalin ƙarfe 2 na dare ne ’yan bindigar suka kai harin, inda daga bisani suka loda ɗaliban da malaman a cikin wata babbar mota da suka ƙwace a yankin.

Daga baya sun jefar da motar a hanya bayan da ya samu matsala, suka kora mutanen zuwa cikin daji.

An kai harin ne kwana huɗu bayan a ranar Litinin ’yan bindiga sun yi garkuwa da ɗalibai 26 makarantar ’yan mata ta GGCSS da ke yankin Maga a Ƙaramar Hukumar Danko Wasagu da ke Jihar Neja — ’yan bindigar na neman kuɗin fansa Naira miliyan 100 a kan ɗaliban.

Aminiya ta ruwaito cewar Gwamnatin Tarayya ta ba da umarnin rufe duk makarantunta na kwana guda 41 da ke faɗin ƙasar nan a sakamakon hare-haren.

Kafin nan gwamnatin jihar Katsina ya rufe ɗauƙacin makarantu, gwamnatin Filato ta rufe ɗauƙacin makarantun ƙananan sakandare, a yayin da gwamnatin Kwara ta rufe wasu makarantu 50 a wasu yankuna saboda tsaro, bayan sace Ɗaliban Makarantar Maga.

Gwamnatin Jihar Neja zargi Hukumomin Makarantar St. da rashin bin umarnin kada a bisa ga makarantar saboda rashin tsaro a yankin, amma hukumomin makarantar suka yi biris da umarnin gwamnatin suka yi gaban kansu wajen buɗe makarantar, lamarin da ya jefa rayuwar dalibai da malaman cikin haɗari.

Idan ba a manta ba, bayan harin Makarantar Maga, Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya umarci Ministan Tsaro Bello Matawalle da ya koma Jihar Kebbi, jami’an tsaro kuma su tabbata sun ceto yaran cikin aminci.

SP Wasiu Abiodun, kakakin ’yan sanda na Jihar Neja, ya tabbatar da harin tare da cewa an tura jami’an tsaron haɗin gwiwa na musamman domin ceto ɗaliban da malamansu.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *