Babu wani addini da matsalar tsaron Nijeriya ta ƙyale — Fafaroma
Shugaban Cocin Katolika na Duniya, Fafaroma Leo XIV, ya musanta zargin cewa ana yi wa Kiristoci kisan kiyashi a Najeriya.
Babban limamin, ya bayyana cewa duk da cewa akwai damuwa dangane da matsalar tsaron Nijeriya, amma babu wani mabiyi na kowanne addini da matsalar ta ƙyale.
“Matsalar tsaron da ake fuskanta a Nijeriya ba Kiristoci kaɗai ta shafa ba, domin ta shafi Musulmi da sauran al’ummomi baki ɗaya,” in ji shi.
Fafaroman ya yi wannan furucin ne yayin da yake zantawa da ’yan jarida a lokacin da yake barin gidansa na Castel Gandolfo a Vatican, inda aka tambaye shi game da tsaron Kiristocin Najeriya, musamman yadda kasashen Yamma ke nuna damuwa.
Ya ce tashin hankalin kasar ya samo asali ne daga ta’addanci, matsin tattalin arziki da kuma rikice-rikicen mallakar ƙasa, ba addini kaɗai ba.
“A wasu yankuna na Najeriya, lallai Kiristoci na cikin haɗari; amma haka lamarin yake ga kowa a ƙasar gaba ɗaya. Ana kashe Kiristoci da Musulmi,” in ji shi, a zantawa da EWTN News.
Sai dai ya akwai buƙatar gwamnatin Najeriya da sauran al’ummomin ƙasar su haɗa kai wajen inganta ’yancin addini na gaskiya, domin kawo ƙarshen tashin hankalin da ake fuskanta
Aminiya ta ruwaito cewa furucin Fafaroman na zuwa ne bayan matakin da Shugaba Donald Trump ya ɗauka kwanan nan na sanya Najeriya cikin jerin Kasashe Masu Fuskantar Barazana saboda zargin take haƙƙin ’yancin addini.
Sai dai gwamnatin Najeriya ta musanta zargin cewa ana yi wa mabiya addinin Kirista kisan kiyashi, tana mai jaddada cewa irin wannan bayani ba ya nuna haƙiƙanin abin da ke faruwa a ƙasar.
Haka zalika, ko a watan Satumba da ya gabata, Sakataren Gwamnatin Vatican, Cardinal Pietro Parolin, ya bayyana matsalar tsaron Najeriya a matsayin rikici na zamantakewa, musamman tsakanin makiyaya da manoma, ba rikicin addini ba kamar yadda wasu suke ɗauka.
A ranar Laraba, Mai bai wa Shugaban Kasa shawara kan tsaro, Nuhu Ribadu, ya jagoranci wata tawaga zuwa Amurka domin musanta zargin yi wa Kiristoci kisan kiyashi a ƙasar.
Tawagar ta gana da Riley Moore, wakilin da Trump ya tura binciko lamarin, inda suka yi tattaunawa mai zurfi game da gaskiyar halin da ake ciki a Najeriya.