Kwamitin Kolin JKS Ya Gudanar Da Taron Karawa Juna Sani Domin Tunawa Da Cika Shekaru 110 Da Haihuwar Hu Yaobang

[ad_1]


Kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin wato JKS, ya gudanar da taron karawa juna sani, domin tunawa da cika shekaru 110 da haihuwar marigayi Hu Yaobang a safiyar yau Alhamis a babban dakin taron jama’a.

Yayin taron, babban sakataren kwamitin kolin JKS, kuma shugaban kasar, kana shugaban kwamitin kolin soja Xi Jinping, ya gabatar da muhimmin jawabi, inda a cikinsa ya ce “Dole ne mu yi koyi da babban ruhin Hu Yaobang, da kyakkyawan salon aikinsa, mu ci gaba da bin burinmu na asali, da kuma kiyaye manufarmu. Mu karfafa kwarin gwiwarmu a kan tarihi, mu tinkari kalubalen tarihi, da kuma ci gaba da inganta dukkan ayyukanmu cikin himma.”

Bugu da kari, Xi ya jadadda cewa, Hu Yaobang ya yi kira da a inganta bude kofa ga waje da yin gyare-gyare a gida, ya sadaukar da kansa a ayyukan bunkasa zamanantar da tsarin gurguzu. Don haka ya kamata dukkan mambobin JKS su yi koyi da shi, wato su tsaya a sahun gaba a zamanin yau, da jajircewa wajen yin gyare-gyare da kirkire-kirkire, da kuma kara zurfafa gyare-gyare a dukkan fannoni, bisa ruhin magance kalubale masu tsanani, ta yadda za a ci gaba da ‘yantarwa, da kuma bunkasa karfin samar da kayayyaki, da karfafawa da kuma inganta kuzari na zamantakewarmu. (Safiyah Ma)

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *