Firaministan Sin Ya Yi Kira Da A Hada Karfi Tare Da Kasashe Masu Tasowa Wajen Kare Moriyar Bai Daya
[ad_1]
Firaministan Sin Li Qiang, ya yi kira ga Sin da Zambiya da su karfafa tsare-tsare da hadin gwiwar mabanbantan sassa, su kuma dunkule tare da gungun kasashe masu tasowa, wajen kare odar tattalin arziki da cinikayya tsakanin kasa da kasa, da goya baya ga daidaito da adalci, tare da kare moriyarsu ta bai daya.
Li Qiang, wanda ya bayyana hakan a Alhamis din nan, ya kara da kira ga Sin da Zambiya da su hada kai da kasar Tanzania, wajen farfado da layin dogo na Tanzaniya zuwa Zambiya.
Li, ya yi kiran ne yayin da yake zantawa da shugaban kasar Zambiya Hakainde Hichilema, bayan saukarsa a birnin Lusaka fadar mulkin Zambiyan a jiya Laraba, inda yake gudanar da ziyarar aiki. (Mai fassara: Saminu Alhassan)
[ad_2]
Source link