’Yan Bindinga Sun Sace Mutane 9, Sun Raunata 1 A Sakkwato
[ad_1]
’Yan bindiga sun kai hari ƙauyen Tarah da ke ƙaramar hukumar Sabon Birni a Jihar Sakkwato a daren ranar Talata.
A lokacin kai harin, sun sace mutane tara tare da jikkata mutum ɗaya.
Tun da jimawa al’ummar Arewacin Jihar Sakkwato na fuskantar hare-haren ‘yan bindiga akai-akai.
An jima ana sace ko kashe mutane a ire-iren waɗannan hare-hare, abin da ya sa yankin ya kasance cikin zaman ɗar-ɗar.
Wannan sabon harin ya faru ne kwanaki kaɗan bayan an tura ‘yan ƙungiyar sa-kai ƙauyen Katsira.
Rashin su ya bar al’ummar Tarah ba tare da kariya ba.
Majiyoyi sun ce matasa sun haɗa kai don tunkarar ’yan bindigar.
Lokacin da aka tuntubi mai magana da yawun rundunar ‘yansandan jihar, DSP Ahmad Rufai, ya ce har yanzu Babban Jami’in ‘Yansanda (DPO) na Sabon Birni bai ba shi cikakken rahoto game da harin ba.
Amma ya ce da zarar ya samu cikakken bayani, zai sanar da manema labarai abin da ya faru.
[ad_2]
Source link