United za ta yi wasanni 6 a jere babu Benjamin Sesko
[ad_1]
Dan wasan gaban Manchester United, Benjamin Sesko zai yi jinyar makonni huɗu, lamarin da zai hana shi buga wa ƙungiyar wasanni shida a jere.
Šeško mai shekaru 22, ba zai samu damar taka leda ba a wasan da United za ta karɓi baƙuncin Everton a Old Trafford mako mai zuwa.
Haka kuma ba zai haska ba a sauran wasannin da za su biyo baya da Crystal Palace, West Ham, Wolves, Bournemouth da kuma Aston Villa.
Ana sa ran dan wasan na ƙasar Slovenia zai dawo cikin ƙungiya ne a lokacin da Manchester United za ta karɓi baƙuncin Newcastle United a gida.
Sesko ya ji raunin ne a wasan da Manchester United ta tashi 2–2 da Tottenham a ranar 18 ga Oktoba, 2025.
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link