Na kusa komawa APC – Gwamnan Taraba
[ad_1]
Gwamnan Jihar Taraba, Agbu Kefas, ya ce zai fice daga jam’iyyar PDP tare da sauya sheƙa zuwa APC a hukumance a ranar Laraba, 19 ga watan Nuwamba.
Ya bayyana haka ne yayin da yake duba aikin gyaran Filin Wasanni na Jolly Nyame da ke Jalingo a ƙarshen mako.
Yayin da yake magana da ’yan jarida, Gwamna Kefas, ya ce ya yanke shawarar ficewa daga PDP ne saboda nemo hanyar da zai amfanar da al’ummar Taraba.
Ya ce: “Zan sauya sheƙa a hukumance daga PDP zuwa APC a ranar 19 ga watan Nuwamba. Wannan sauyi zai amfanar da al’ummar Taraba.”
Ya ƙara da cewa ana ci gaba da shirye-shiyen bikin tarbarsa.
Da aka tambaye shi ko akwai wani sharaɗi da aka gindaya masa kafin ya sauya sheƙa, ya ce babu ko ɗaya.
Mambobin Majalisar Zartarwa ta jihar sun nuna cikakken goyon bayansu ga gwamnan.
Kwamishinan Kimiyya da Fasaha, Muslim Aruwa, wanda ya yi magana a madadin sauran kwamishinoni, ya ce dukkanin muƙarraban gwamnan za su bi shi zuwa APC.
Ya ce: “Gwamna shi ne shugabanmu, duk inda ya je muna tare da shi.”
Aruwa, ya bayyana cewa shiga jam’iyyar da mulkin tarayya zai samar wa jihar ci gaba.
Ya ƙara da cewa: “Wannan sauya sheƙa na mutanen Taraba ne baki ɗaya, kuma muna tare da shi ɗari bisa ɗari.”
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link