Tinubu Ya Aika Wakilai Don Tattaunawa Da Birtaniya Kan Dawo Da Ekweremadu Nijeriya

[ad_1]


Wakilan Shugaba Bola Tinubu, ƙarƙashin jagorancin Ministan Harkokin Waje, Yusuf Tuggar, ta fara tattaunawa da hukumomin Birtaniya kan ci gaba da tsare tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawa, Ike Ekweremadu.

Wakilan na buƙatar a ba da damar dawo da Ekweremadu Nijeriya domin ya ci gaba da zaman gidan yari a gida, maimakon a ci gaba da tsare shi a Birtaniya.

Bayan isarsu Birtaniya, wakilan sun gana da ministocin harkokin waje da na shari’a, tare da tsara wasu taruka da manyan jami’ai da ke da hannu a lamarin.

Mai magana da yawun ministan harkokin waje, Alkasim AbdulKadir, ya tabbatar da cewa ana ci gaba da tattaunawa, inda ya bayyana cewa an gabatar da buƙatar musayar fursunoni domin Ekweremadu ya dawo Nijeriya.

A cewar majiyoyi daga ma’aikatar harkokin waje, gwamnati na ganin wannan mataki zai bai wa Ekweremadu damar samun kulawar likitoci likitocinsa, tare da sauƙaƙa wa gwamnati da iyalinsa damuwar da ke tattare da zamansa a ƙasar waje.

An kuma bayyana cewa gwamnatin Tinubu tana ƙoƙarin amfani da wannan tattaunawa wajen ƙarfafa dangantaka da Birtaniya, musamman wajen harkokin shari’a, musayar bayanan tsaro, da kula da ‘yan Nijeriya da ke fuskantar matsaloli a ƙasashen waje.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *