Wani mutum ya rasu a gidan karuwai bayan ziyartar ’yan mata
Wani mutum da ba a gano sunansa ba ya mutu bayan da ya shiga wani gidan karuwai domin ganawa da ’yan mata masu zaman kansu a birnin Fatakwal.
Lamarin ya faru ne a ranar Lahadi, inda rahotanni suka ce mamacin ya shiga gidan karuwai ne domin yin hulɗa da ’yan mata, sai dai ba a tabbatar da abin da ya jawo mutuwarsa ba.
Jami’ar Hulɗa da Jama’a ta Rundunar ’Yan Sandan Jihar Ribas, SP Grace Iringe-Koko, ta tabbatar da faruwar lamarin a ranar Litinin, inda ta ce an miƙa batun zuwa Sashen Binciken Manyan Laifuka na Jihar (SCID) domin gudanar da cikakken bincike.
Wasu majiyoyi daga cikin gidan karuwan sun bayyana cewa wani ma’aikacin otal ɗin da ke kula da wurin ya yi faɗa da mamacin kafin daga bisani ya yanke jiki ya faɗi ya mutu.
Majiyar ta ƙara da cewa an garzaya da mutumin asibiti domin ba shi agajin gaggawa, amma daga bisani likitoci suka tabbatar da mutuwarsa.
Rahotanni sun ce an kama wani mutum daga cikin gidan matan da ake zargi da hannu a lamarin, kuma rundunar ’yan sanda ta jihar ta ta fara bincike a kai.
SP Grace Iringe-Koko ta kuma tabbatar da cewa an kama mutum ɗaya da ake zargi, kuma sashen ’yan sanda na Azikiwe ya miƙa shari’ar zuwa SCID domin gudanar da bincike mai zurfi.
Sai dai bayan faruwar lamarin, an lura dukkan ’yan mata masu zaman kansu da ke yawo a cikin da wajen gidan karuwan sun yi layar zana.