Kamfanonin Kasa Da Kasa Na Fatan Yin Amfani Da Damammaki Na Shirin Raya Kasa Na Shekaru Biyar–Biyar Karo Na 15 Na Sin
[ad_1]
A matsayin babban taron tattalin arziki na farko bayan taron cikakken zama na 4 na kwamitin tsakiya na 20 na jam’iyyar JKS, shugabannin kamfanoni masu yawa a bikin CIIE sun yaba wa damar ci gaban da shirin raya kasa na shekaru biyar-biyar karo na 15 ke kawo da kuma budaddiyar fuskar Sin, wakilan CMG sun zanta da wasu shugabannin kamfanonin kasa da kasa dake da sassa a kasar Sin, bari mu ga ra’ayoyinsu game da hakan.
Shehun malami a cibiyar nazarin harkokin Asiya ta jami’ar kasar Singapore, Kishore Mahbubani ya bayyana cewa, kasar Sin ce kasa daya tilo a duniya da ta dauki matakin shirya bikin baje kolin kayayyakin da ake shigarwa kasarta, yana mai bayyana hakan a matsayin mai matukar ma’ana.
Shehun malamin ya kara da cewa, “A ganina, kasar Sin tana da idon basira, la’akari da yadda take aiwatar da shirye-shiryen raya kasa na shekaru biyar-biyar, matakin da ya sa kason kasar a duniya ta fannin sana’o’in kere-kere ya yi ta karuwa, adadin ake sa ran zai kai 45% ya zuwa 2030, maimakon yadda ya kasance a kaso 5% kawai a shekarar 2000.
An baje kolin sabbin kayayyaki da fasahohi da ma hidimomi da yawansu ya kai har 461 a gun bikin baje kolin kayayyakin da ake shigowa da su kasar Sin na kasa da kasa karo na takwas da ke gudana a birnin Shanghai na kasar Sin (CIIE). Amma me ya sa kamfanoni masu jarin waje suke ta kokarin baje kolin sabbin kayayyakinsu a gun bikin?
Zhong Zhonglin, shugaban Nippon Paint reshen Sin ya ce, “Bayan an kammala wannan cikakken zama, mun ga manufofin Sin sun kara budewa ga ketare, kuma sun fi karbar jarin kasashen waje. Muna da kwarin gwiwa sosai game da kasuwar Sin.”
Zhang Lei, mataimakiyar shugaban sashen yada labaru na kamfanin BaySystems reshen Sin da yankin arewa maso gabashin Asiya, ta kara da cewa, “A cikin shekaru 140 da suka gabata, mu kasance a nan ba mu taba barin ba, ko a lokacin wahala ko a’a. Wannan yana nuna irin kauna da alkawarin da wannan tsohon kamfanin Jamus mai shekaru 100 ke da su ga kasar Sin.”
A game da hakan, Frank Hammes, babban darektan kamfanin IQAir na kasar Switzerland ya bayyana cewa, bikin CIIE tamkar dakin gwaje-gwaje ne a gare mu, inda ban da baje kolin sabbin nasarorinmu, muna kuma iya samun martani daga masu sayayya.
Shi kuma Mr. Yu Feng, babban darektan kamfanin Honeywell da ke kula da harkokin kasar Sin, ya ce, masu sayayya wadanda da wuya a biya bukatunsu, alheri ne ga kamfanonin kirkire-kirkiren fasahohin zamani, sabo da su ne suke taimakawa wajen kirkiro sabbin fasahohin zamani.
“Za mu ci gaba da zuba jari a Sin har na karni 1”, “Za mu kara kusan shaguna 100 a Sin”. Nicolas Hieronimus shugaban kamfanin L’Oréal da Sandeep Seth, babban ma’aikacin kamfanin Tapestry sun fadi hakan yayin zantawar da wakilin CMG ya yi musu.
Hieronimus ya ce, “Sin ita ce kasuwa ta biyu mafi girma a duniya gare mu, kuma cibiyar kirkira ce mai karfi.” Seth kuma ya ce, “Kasuwar Sin ta zama filin gwajin sabbin dabaru.”
Wadannan kalamai sun nuna yadda suke amincewa da CIIE, tare da bayyana niyyar su ta ci gaba da fadada kasuwancinsu a Sin. (Lubabatu Lei da Amina Xu)
[ad_2]
Source link