LABARAN RANAR ALHAMIS 07-08-2025
Labaran Safiyar Alhamis 07/08/2025CE – 13/02/1447AH Ga Takaitattun Labaran.
Shugaba Tinubu ya jajanta wa al’ummar Ghana kan mutuwar ministoci.
Shugaba Tinubu ya bayar da umarnin samar da tsarin kula da lafiya kyauta ga masu ƙaramin ƙarfi da suka yi ritaya a ƙarƙashin shirin fansho na karo-karo.
Shugaba Tinubu ya taya Nafisa, Rukayya, Hadiza murnar samun nasarar zama gwanaye a gasar turanci ta Duniya.
Shugaban EFCC, Olukoyede ya ce galibin rukunin gidajen da aka fara amma aka yi watsi da su a Abuja na ma’aikatan gwamnati ne da suka mallaka da kudaden sata.
Gwamnatin Kano ta ce za ta bai wa iyalan ƴan wasan nan 22 kuɗaɗe da filaye a matsayin gudummawa bayan rasuwarsu a kan hanyar komawa gida daga jihar Ogun.
Wani soja wanda ba a daɗe da yaye su ba, Dauda Dedan, ya yi layar zana bayan zargin sa da kashe wani ɗansanda, Aaron John, ta hanyar caka masa wuƙa a Jalingon jihar Taraba.
Sojoji sun Kama mai yi wa Boko Haram safarar Man Fetur a jihar Borno.
Mataimakin Gwamnan Jihar Taraba, Alhaji Aminu Alkali, ya yi ɓatan dabo inda ya shafe tsawon watanni takwas ba tare da an gan shi ba.
Rundunar ƴan sandan Kano ta shawarci al’umma su kai mata rahoton duk wani ɗan sanda da suke zargin yana karɓar cin hanci don haɗa baki ko rufa asirin wasu ɓata-gari ko masu aikata laifi a yankunansu.
Hukumar Kwastam ta kama Tankar mai dauke da buhunan shinkafa a Kaduna.
Sarkin Kano na 16 Muhammadu Sanusi II ya zargi ƴan siyasar Najeriya da aikata cin hanci da rashawa sabida “rashin tarbiyya tun daga tasowarsu”.
Mahukuntan Abuja sun fatattaki mabarata 273, sun kama ababen hawa 670 a cikin watanni hudu
Jami’an ‘yan sanda, sun kama fitattacen dan fafutuka, kuma tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa, Omoyele Sowore.
Hukumar WAEC ta rufe shafin duba jarabawar WASSCE 2025.
Faransa na fama da bala’in gobarar daji ‘mafi muni a tarihi’.
Ƙasar Italiya za ta gina gada mafi tsawo a duniya.
Manchester United ta tuntuɓi Brighton kan ɗanwasan ta Carlos Baleba.
Rasha ta ce ana samun ci gaba a tattaunawar tsagaita wuta a yaƙin Ukraine.
Ɗan wasa Alexander Isak an faɗa masa ya yi atisaye shi kaɗai a Newcastle United saboda farautarsa da Liverpool ke ci gaba da yi.
Inter Milan na duba yiyuwar ɗauko ɗan wasan Manchester United Sancho, idan ta kasa samun ɗan wasa Ademola Lookman, daga Atalanta.
Sources.
1. BBC Hausa.
2. Premium Times Hausa.
3. RFI Hausa.
4. Leadership Hausa.
5. Aminiya.
6.Hausa forum
source