’Yan bindiga sun sace mata 5 a ƙauyen Kano
[ad_1]
’Yan bindiga sun kai hari a Jihar Kano a daren Lahadi, inda suka yi garkuwa mata biyar ciki har da masu shayarwa.
Wani ganau ya ce ’yan bindigar sun kai harin ne a ƙauyen ’Yan Kwada da ke cikin yankin Faruruwa a Karamar Hukumar Shanono da ke Shiyyar Kano ta Arewa.
Wani mazaunin yankin ya shaida wa Aminiya cewa dandazon maharan sun yi dirar mikiya a garin ne ɗauke da muggan makamai, inda suka yi ta harbe-harbe tare da shiga gidaje suna yin awon gaba da mutane.
“Sun zo kamar yadda suka saba, suna harbi a iska suna karya ƙofofi. Sun tafi da mata biyar, ciki har da masu shayarwa,” in ji majiyar.
Sai dai ya ce daga cikin matan da aka sace, biyu sun tsere sun dawo, yayin da ragowar ukun ke hannun ’yan bindigar.
Harin na daren Lahadi na zuwa ne bayan mako guda da sojoji suka hallaka ’yan bindigar kimanin 19 a yankin.
Mutanen Faruruwa da sauran kauyuka da ke kan iyakar Kano da Katsina na ci gaba da rayuwa cikin fargaba sakamakon hare-haren ’yan bindiga da ke faruwa lokaci zuwa lokaci.
A sakamakon tsananin rashin tsaro, an ruwaito cewa yawancin ƙauyuka sun zama kufai, inda mazauna suka tswre zuwa garin Faruruwa ko kuma zuwa birane don tsira da rayukansu.
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link