Tinubu Ya Umarci Ma’aikatar Ilimi Ta Kawo Ƙarshen Yajin Aikin ASUU

[ad_1]


Ministan Ilimi, Dr. Tunji Alausa, ya bayyana cewa Shugaba Bola Tinubu ya ƙwanƙwashi Ma’aikatar Ilimi don tabbatar da cewa, ɗaliban jami’a suna ci gaba da karatunsu ba tare da wani cikas ba, yana mai cewa, Gwamnatin Tarayya tana yin duk abin da ya dace don hana Ƙungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU) tsunduma wani yajin aiki a nan gaba.

Da yake magana da manema labarai na Fadar Shugaban Ƙasa, Abuja, a ranar Talata, Ministan ya ce Shugaba Tinubu ya umarce shi da ya nemo mafita mai ɗorewa ga duk wata matsala da ka iya kawo cikas ga ayyukan ilimi a manyan makarantun ƙasar nan.

“Kamar yadda na gaya muku, Shugaban Ƙasa ya umarce mu da cewa, ba ya son ASUU ta sake shiga wani yajin aiki, kuma muna yin duk abin da ya dace don tabbatar da cewa ɗalibanmu suna makaranta,” in ji Alausa. “Yajin aikin na kwanan nan da suka yi na kimanin kwanaki shida bai dace ba don muna kan magana da su.”

Ya ƙara da cewa: “Mun cika dukkan buƙatunsu. Yanzu mun koma teburin tattaunawa, yanzu haka na zo wurin shugaba Tinubu ne don zayyana masa inda muka tsaya da ASUU.”

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *