Tsohon Mataimakin Shugaban Amurka Dick Cheney ya mutu

[ad_1]



Tsohon Mataimakin Shugaban Amurka, Dick Cheney, ya rasu yana da shekaru 84 a duniya.

Cheney shi ne mataimakin shugaban ƙasa na 46, wanda ya yi aiki tare da tsohon shugaban ƙasa, George W. Bush a wa’adin mulki biyu daga shekarar 2001 zuwa 2009.

A cewar iyalansa, marigayin ya rasu bayan doguwar jinyar da ya yi fama da ita sakamakon ciwon huhu da na zuciya da jijiyoyin jini.

Dick Cheney, wanda aka san shi da tsananin ra’ayin mazan jiya, yana daga cikin mataimakan shugabanni mafi tasiri a tarihin Amurka.

Ya taka muhimmiyar rawa wajen yaƙin Iraki, tare da goyon bayan amfani da na’urorin leƙen asiri da bincike mai tsanani a matsayin martani ga harin ta’addanci na ranar 11 ga Satumba, 2001.

Bayan ya bar ofis, Cheney ya zama ɗaya daga cikin masu sukar salon jagorancin shugaban ƙasa Donald Trump a wa’adin mulkinsa na farko, musamman bayan ’yarsa, Liz Cheney, ta zama jigo cikin ’yan jam’iyyar Republican da suka fito fili suna sukar Trump, lamarin da ya zamo sila dakatar da shi daga jam’iyyar.

Liz Cheney ta kasance ɗaya daga cikin ’yan jam’iyyar da suka soki matakin magoya bayan Trump na tayar da tarzoma a ginin Majalisar Dokoki ta ƙasar (Capitol) bayan shan kaye a zaɓen ranar 6 ga Janairu, 2021.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *