Shugaba Xi Ya Mika Sakon Taya Murnar Bude Babban Gidan Tarihi Na Kasar Masar

[ad_1]


Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya mika sakon taya murnar bude babban gidan tarihi na kasar Masar ga shugaba Abdel-Fattah al-Sisi. Cikin sakon nasa na jiya Asabar, shugaba Xi ya ce “Albarkacin bude babban gidan tarihin na Masar, ina fatan mika sahihin sakon taya murna ga shugaba Abdel-Fattah al-Sisi da al’ummun kasar. Na yi imanin cewa babban gidan tarihin na Masar zai bar wata muhimmiyar alama a tarihin al’adun Masar, tare da taka rawar gani wajen karewa, da kuma gadar da dadaddiyar wayewar kan kasar”.

Kazalika, shugaba Xi ya jaddada cewa, Sin da Masar na da dogon tarihi na kawance. Kuma a shekarun baya bayan nan, cikakkiyar dangantaka bisa manyan tsare-tsare tsakanin sassan biyu ta kara bunkasa, inda sassan ke musayar al’adu masu ban sha’awa. Ya ce baje kolin tsofaffin abubuwan wayewar kai na Masar da aka gudanar a gidan adana kayan tarihi na birnin Shanghai ya gudana cikin nasara, kana wata tawagar hadin gwiwa ta masu hako kayan tarihi ta Sin da Masar, na aiki don zakulo kayayyakin tarihi masu tsawon tarihi na wayewar kan Masar dake boye a karkashin dalar duwatsu ta “Saqqara”.

Ya ce “Muna farin ciki da ganin tsofaffin kasashenmu masu tsofaffin wayewar kai suna kara yin mu’amala da hadin-gwiwa, kuma al’ummun kasashen biyu na kara fahimtar junansu.”

Shugaba Xi ya kara da cewa, a halin da ake ciki yanzu, duniya na fuskantar sauye-sauye irin wadanda ba a taba gani ba kuma cikin sauri. Don haka, kamata ya yi kasashen biyu masu dadaddun wayewar kai su zurfafa koyi da juna, da shigar da sabon kuzari cikin gina cikakken salon hadin kai, bisa manyan tsare-tsare tsakaninsu, kana su tattaro karfin wayewar kai don gina al’umma mai makomar bai daya ga dukkanin bil’adama.

A wani ci gaban kuma, wakilin musamman na shugaban kasar Sin Xi Jinping wato ministan raya al’adu da yawon bude ido na kasar Sun Yeli, ya halarci bikin bude babban gidan adana kayan tarihin na GEM bisa gayyatar gwamnatin Masar. Kafin bikin, shugaba al-Sisi ya gana tare da gudanar da gajeriyar tattaunawa da Sun Yeli. (Saminu Alhassan)

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *