Matsalar tsaro na iya hana mu ci gaba da rijistar masu zabe a Borno – INEC

[ad_1]



Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta ce matsalar tsaro na iya hana ta gudanar da aikin rijistar masu zabe a kananan hukumomin jihar Borno guda hudu.

Kananan hukumomin da lamarin zai iya shafa su ne Abadam, Guzamala, Marte da Kala-Balge.

Bayanin hakan dai ya fito ne daga bakin Kwamishinan Zabe na jihar, Abubakar Ahmad Ma’aji a jawabin sa ga manema labarai a Maiduguri, a wani vangare na shirye-shiryen fara gudanar da aikin rijistar masu kada kuri’a a ranar Litinin da ke tafe.

A cewar shi, INEC ta mayar da rijistar masu zaben a karamar hukumar Abadam zuwa kan hanyar Baga, daura da ofishin Yerwa Peace.

Kazalika, ya ce a karamar hukumar Guzamala an mayar da wurin yin rajistar sashen kashe gobara na rukunin gidaje 1,000.

Ya ce sauran kananan hukumomin kamar karamar hukumar Kala-Balge an mayar da aikin ya koma zuwa  makarantar firamare ta Goni Kachalari da ke birnin Maiduguri.

Shi kuma aikin rijistar masu kada kuri’a na qaramar hukumar Marte an mayar da shi ya zuwa Kachamai, wadanda dukkansu suna cikin birnin Maiduguri ne.

Don haka kwamishinan ya yi kira ga mutanen kananan hukumomin da su yi hakuri da wannan canji da aka samu, inda ya ce an yi ne da kyakkyawar manufar da duk wanda abin ya shafa zai samu rijistarsa cikin kwanciyar hankali.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *