An Samu Ingantuwar Yanayin Iska Da Ruwa Cikin Watanni 9 Na Farkon Bana A Sin
[ad_1]
Kakakin ma’aikatar kula da muhalli ta kasar Sin Pei Xiaofei ya bayyana a yau cewa, yanayin ruwa da na iska a kasar ya ci gaba da ingantuwa a cikin watanni 9 na farkon bana.
A cewarsa, matsakaicin nauyin burbushin abubuwan dake cikin iska na PM2.5, wanda shi ne muhimmin ma’aunin gurbatar iska, ya tsaya kan microgram 26 kan kowane cubic mita, a cikin birane ko garuruwan Sin 339, daga watan Janairu zuwa na Satumba, wannan ya nuna cewa an samu raguwar ma’aunin da kaso 5.1 kan mizanin shekara-shekara.
Haka kuma, cikin watanni 9 na farkon bana, an samu ingantacciyar iska a kaso 87.6 na kwanakin, wanda ya karu da maki kaso 1.8 kan na bara.
Ma’aikatar ta kuma bayyana cewa a wannan lokaci, an kasa kaso 89 na matattarar ruwa 3,641 dake karkashin kulawar kasar Sin bisa matakin inganci daga 1 zuwa III, wanda ke nuna ingancinsu, wanda ya karu da kaso 0.5 kan na makamancin lokacin a bara. (Mai fassara: FMM)
[ad_2]
Source link