Paul Biya mai shekara 92 ya lashe zaɓen Kamaru
[ad_1]
Shugaba Paul Biya na Jamhuriyar Kamaru ya sake lashe zaɓen Shugaban Ƙasar domin fara wa’adi na takwas na shekara bakwai.
Kotun Kundin Tsarin Mulkin ƙasar ta sanar cewa Mista Paul Biya mai shekaru 92 ya samu nasara ne bayan ya samu 53.66 na kuri’un da aka jefa a yayin da babban abokin hamayyarsa, Issa Tchiroma Bakary ya samu kashi 35.19.
Da haka biya zai ci gaba da mulki inda zai kammala sabon wa’adin yana dan shekara 99.
Zuwa ƙarshen wa’adin, Biya wanda ya shekara 43 a gadon mulki tun 1982 zai cika shekara 50 a kan mulki.
A halin yanzu shi ne shugaban kasa mai ci mafi tsufa a duniya.
Shi ne kuma zaɓaɓɓen shugaban ƙasa na biyu a tarihin Kamaru tun bayan samun ’yanci daga Turawan mulkin mallaka.
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link