An kama mutum 25 kan zargin shirya auren jinsi a Kano
[ad_1]
Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta samu nasarar cafke wasu mutum 25 da ake zargi da shirya auren jinsi a samamen da ta kai wani wurin shagali a jihar.
A cewar hukumar, an kama mutanen ne da yammacin Asabar a wani wurin taro da ke kan titin Hotoro Bypass a ƙaramar hukumar Tarauni.
Mataimakin Kwamanda Janar na Hukumar Hisbah mai kula da ayyuka na musamman, Sheikh Dokta Mujahid Aminuddeen Abubakar, ne ya tabbatar da kama waɗanda ake zargin a ranar Lahadi.
Ya bayyana cewa samamen na zuwa ne bayan bayanan sirri da hukumar ta samu daga wani mai kishin al’umma.
Ya bayyana cewa bayanan sirrin sun nuna cewa wani mai suna Abubakar Idris yana shirin auren wani matashi, lamarin da ya sa jami’an Hisbah suka bazama zuwa wurin da taron ke gudana.
Ya ƙara da cewa daga cikin wadanda aka kama akwai maza 18 da aka bayyana a matsayin ’yan daudu, da kuma mata 7 daga unguwanni daban-daban ciki har da Sheka, Yar Gaya da Kofar Nasarawa.
Dokta Mujahid ya ce a halin yanzu duk ababen zargin suna hannun hukumar, kuma za a gurfanar da su gaban kotu da zarar an kammala bincike.
Ya yi kira ga iyaye da su kula wajen inganta tarbiyyar ’ya’yansu, tare da roƙon jama’a da su rika sanar da hukumar Hisbah ko hukumomin tsaro idan sun ga wani abin da ke da ɗaukar hankali.
Mataimakin kwamandan ya sake jaddada ƙudirin hukumar na ci gaba da tabbatar da ɗabi’a ta gari da kare mutuncin Kano a matsayin jihar da aka sani kan ginshiƙin ladabi da ƙa’idojin addinin Musulunci.
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link