Gwamnonin PDP na yanzu za su rusa mana jam’iyya — Wike
Ministan Babban Birnin Tarayya , Nyesom Wike, ya yi gargadin cewa irin yadda gwamnonin jam’iyyar PDP ke tafiyar da al’amuranta a yanzu, zai iya sanadin rushewar jam’iyyar.
Wike, ya bayyana haka ne a lokacin da yake hira da ’yan jarida a Abuja ranar Juma’a, inda ya zargi gwamnonin PDP da gaza magance rikicin jam’iyyar yadda ya kamata.
Rahotanni sun nuna cewa akwai rashin jituwa tsakanin Wike da gwamnonin PDP.
Jam’iyyar na shirin gudanar da babban taronta na kasa a watan Nuwamba a birnin Ibadanna Jihar Oyo, amma wasu rahotanni na cewar magoya bayan Wike na ƙoƙarin hana gudanar da taron.
A kwanakin baya, Sakataren Jam’iyyar na Kasa, Samuel Anyanwu, ya zargi Kwamitin Gudanarwa na Jam’iyyar naKasa (NWC) da yin amfani da sa hannunsa na bogi wajen aike wa INEc wasiƙa don sanar da shirin gudanar da taron.
Sai dai wasu shugabannin jam’iyyar sun ce Anyanwu yana aiki ne bisa umarnin Wike.
A yayin tattaunawar da ya yi da ’yan jarida, Wike ya ce: “Ban faɗa tun farko cewa tarkon da kuke saka wa kanku zai kama ku ba? Na faɗa tun da wuri, irin yadda waɗannan gwamnonin ke tafiyar da jam’iyyar, za su kashe ta ne.
“Kuna gudanar da taron jam’iyya, kuna kiran mutane manyan jam’iyya, amma kun bar ni saboda ba gwamna ba ne, ta yaya za ku ci gaba a haka?”
Wike ya kuma nesanta kansa daga masu goyon bayan tsohon Ministan Harkoki na Musamman, Tanimu Turaki, a matsayin sabon shugaban jam’iyyar.
“Ban san wani abu game da Tanimu Turaki kan zama shugaban jam’iyya ba. Wataƙila zai zama shugaban wani bangare daban ne, ba PDP dana sani ba,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa tun da farko ya yi hasashen wasu ’ya’yan jam’iyyar za su fice daga cikinta.
“Tun farko na faɗa cewa idan abubuwa suka ci gaba da tafiya a haka, PDP za ta rika yin asara. Ana tafiyar da abubuwa bisa kuskure, kuma yanzu kowa yana gani. Abin kunya ne,” in ji shi.
“Duk abin da na faɗa a da yanzu yana faruwa,” a cewar Wike.