’Yan uwana 8 sun rasu a fashewar tanka a Neja — Wani Mutum
[ad_1]
Wani mutum mai suna Mallam Surajo Muhammad Shehu ya rasa ’yan uwansa takwas, lokacin da tankar mai ta yi bindiga a garin Essa da ke kan hanyar Agaie zuwa Bida, a Jihar Neja.
Lamarin ya auku a ranar Talata, wanda aƙalla mutum 28 ciki har da mata da ƙanana yara, suka rasa rayukansu lokacin da tankar ta kife kuma ta kama da wuta yayin da jama’a ke ƙoƙarin ɗibar mai.
Wasu da dama sun ji rauni kuma an garzaya da su Asibitin Gwamnatin Tarayya (FMC) da ke Bida.
Shehu, ya ce mata ne suka fi mtuuwa saboda maza sun tafi gona lokacin da lamarin ya faru.
Ya zargi mazauna yankin da ƙin bin gargaɗin da aka sha yi musu kan hatsarin ɗibar mai daga tankar da ta kife.
Hakimin Essa, Alhaji Adamu Bagudu, ya tabbatar da cewa an binne mutum 28, ciki har da mata 24.
Ya ce an sha gargaɗin jama’a kan hatsarin wannan ɗabi’a, amma talauci da wahalar rayuwa ya sa mutane yin watsi da igargaɗin
Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Jihar Neja (NSEMA), ta ce aƙalla mutum 80 lamarin ya shafa, inda aka kai wasu 17 Abuja domin samun kulawa ta musamman.
Gwamnan Gombe kuma Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin Arewa, Inuwa Yahaya, ya bayyana alhininsa kan lamarin tare da kiran gwamnati da ta ƙara tsaurara matakan tsaro da kuma gyaran hanyoyi.
Majalisar Wakilai ta Ƙasa ta kuma roƙi Gwamnatin Tarayya da ta gaggauta gyara hanyar Bida zuwa Agaie wadda ke janyo salwantar rayukan mutane.
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link