Kotu ta aike da mutumin da ake zargi da satar yaran Kano yana kaiwa Delta zuwa gidan gyaran hali
[ad_1]
Babbar Kotun Jihar Kano a ranar Talata ta bayar da umarnin aikewa da Ogugua Christopher zuwa gidan gayarn hali bisa zarginsa da hannu a sata da kuma safarar yara daga jihar Kano zuwa kudancin Najeriya.
Ana dai zargin mutumin ne da mallakar wani gidan marayu a jihar Delta ba bisa ka’ida ba, sannan yana amfani da shi wajen ajiye yaran da ake zargin na sata ne a ciki.
Hukumar Hana Fatucin Mutane ta Kasa (NAPTIP) ce dai da gurfanar da Christopher tare da wasu abokar harkallarsa su biyu, Hauwa Abubakar da Nkechi Odlyne, wadanda su ba su je kotun ba a ranar.
Alkalin kotun, Mai Shari’a Amina Adamu ce ta bayar da umarnin kullewar yayin fara sauraron shari’ar, bayan sauraron bukatar lauyan masu kara, Salisu Muhammad Tahir da na wanda ake karar, Gideon Uzo.
Daga nan ne kuma kotun ta dage ci gaba da sauraron karar zuwa ranar 27 ga watan Oktoba inda ake sa ran za a gurfanar da Christpher tare da sauran wadanda ake zargin.
An dai kama Chrispoher ne bayan wani samame da jami’an hukumar ta NAPTIP suka kai gidan nasa da ke jihar Delta sannan suka ceto yara takwas da ake zargin ya sace su daga Kano sannan ya kai su gidan marayun nasa da ke Asaba, babban birnin jihar ta Delta.
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link