Gwamnatin Kano ta shirya ɗaurin auren ma’aurata 2,000




Gwamnatin Jihar Kano ta umurci Hukumar Hisba ta jihar da ta fara shirye-shiryen ɗaurin auren ma’aurata aƙalla 2,000 a ƙarƙashin shirinta na ɗaurin auren gata.

Mataimakin babban Kwamandan hukumar, Sheikh Mujahid Aminudeen ya shaida wa kafar PUNCH a wata tattaunawa ta wayar tarho a ranar Alhamis, inda ya ce nan ba da daɗewa ba hukumar za ta fara shirin don ganin an samu nasarar gudanar da taron bikin.

“Muna shirin gudanar da ɗaurin auren wani rukunin ma’aurata guda 2,000 kamar yadda gwamnatin jihar ƙarƙashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf ta umarta,” in ji shi.

Duk da cewa, babban kwamandan bai bayyana ainihin ranar da za a gudanar da babban taron ba, ya ce akwai hanyoyin da za a bi wajen gudanar da ɗaurin auren.

A cewarsa, duk ma’auratan da suka yi rijistar dole ne su je a duba lafiyarsu domin a tabbatar da lafiyarsu domin a yi musu gwajin cutar ƙanjamau da ciwon hanta da gwajin miyagun ƙwayoyi da dai sauransu.

“Duk ma’auratan da za suke da sha’awar shiga tsarin auren dole ne su yi rajista kafin su shiga taron ɗaurin auren da gwamnati ta shirya.

Sakamakon binciken likitan kuma wani ɓangare ne na tsarin da ake buƙata na gudanar da bukukuwan auren, kuma ya zama dole saboda duk wanda bai gabatar da kansa ba don tantancewar za a kore shi, kai tsaye,” in ji shi.




Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *