Fashewar tukunyar gas ya haddasa gobara a jami’ar Gombe

[ad_1]



Wata gobara da ta tashi a daren Alhamis ta lalata wani ɓangare na ɗakin kwanan dalibai mata a Jami’ar Jihar Gombe, tare da jikkata dalibai uku.

Ana zargin gobarar ta tashi ne sakamakon fashewar gas ɗin girki a wani ɓangare na ɗakin kwanan da ke cikin harabar jami’ar.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin a wata hira ta wayar tarho da wakilinmu a ranar Juma’a, Jami’in Hulɗa da Jama’a na Hukumar Kashe Gobara ta Kasa, reshen jihar, Bashir Mu’azu, ya bayyana lamarin da cewa abin takaici ne.

“Lamarin ya faru ne sakamakon fashewar gas ɗin girki. Binciken farko ya nuna cewa daliba ce ta bar girki ba tare da kulawa ba,” in ji Muazu.

Sai dai ya bayyana cewa babu wanda ya rasa ransa, sai dai an kai dalibai uku asibiti.

“Wasu an kwantar da su a asibiti saboda firgici, wasu kuma saboda shakar hayakin gobarar,” in ji shi.

Wakilinmu ya kuma gano cewa a kwanan nan ne jami’ar ta ɗage dokar hana amfani da tukunyar gas a cikin ɗakunan kwana daliban.

A baya dai da risho mai amfani da kananzir kawai hukumar ta amince dalibai su yin amfani da shi saboda fargabar hatsari.

Wasu daga cikin daliban da suka yi magana da wakilinmu da suka bukaci a boye sunayensu sun nuna rashin jin daɗi kan yadda aka tafiyar da lamarin, suna zargin rashin kayan aikin kashe gobara a cikin jami’ar.

“Da hukumar kashe gobara ta jami’a tana aiki yadda ya kamata, da gobarar ba ta yi muni haka ba,” in ji ɗaya daga cikin daliban.

Ƙoƙarin jin ta bakin Jami’in Hulɗa da Jama’a na Jami’ar Gombe, Hadu Naphtali, ya ci tura, domin bai amsa kira ko saƙon kar-ta-kwanan da wakilnmu ya aike masa ba har zuwa lokacin hada wannan rahoton.

A halin yanzu, Kwamandan Hukumar Kashe Gobara a jihar, DCF S.M. Sulaiman, ya shawarci shugabannin jami’ar da su gaggauta dawo da dokar hana amfani da tukunyar gas a ɗakunan kwana don kauce wa afkuwar irin wannan iftila’in a nan gaba.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *