NAPTIP ta kama mahaifin da ke ƙoƙarin safarar ’yarsa zuwa Iraƙi ci-rani
[ad_1]
Hukumar Yaƙi da Safarar Mutane ta Ƙasa (NAPTIP) ta ce ta kama akalla mutane biyar da ake zargi da safarar mutane tare da ceto mutane 24 a Filin Jirgin Sama na Ƙasa Nnamdi Azikiwe, Abuja.
Hukumar ta ce daga cikin wadanda aka cafke ɗin, har da wani uba da ya yi ƙoƙarin safarar diyarsa zuwa Baghdad, babban birnin ƙasar Iraq.
Jami’in Yaɗa Labarai na NAPTIP, Vincent Adekoye, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba.
Wannan na faruwa ne a daidai lokacin da ake ƙara nuna damuwa kan yawaitar safarar mutane, da kuma musamman waɗanda ke yin ƙaura suna barin ƙasar.
A cewar Adekoye, aikin da aka gudanar bayan samun sahihan bayanan sirri, Darakta Janar ta hukumar, Binta Adamu Bello ce ta jagorance shi.
Ya bayyana cewa cikin waɗanda aka kama akwai wani tsohon babban jami’in tsaro, wanda ake zargin babban mamba ne a cikin ƙungiyar masu safarar mutane a yankin Kudu maso Yammacin Najeriya.
Sanarwar ta ce, “A wani babban farmaki da ba a taɓa yin irinsa ba, wanda ya zo ba tare da an shirya ba, Darakta Janar na Hukumar Hana Safarar Mutane ta Ƙasa, Binta Adamu Bello, a yau (Laraba) ta jagoranci wani babban aiki na musamman a Filin Jirgin Sama na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja, wanda ya kai ga ceto mutane 24 da ake ƙoƙarin yin safararsu da kuma kama mutane biyar da ake zargi da safarar mutane.”
“Cikin waɗanda aka kama a filin jirgin sama akwai wani tsohon jami’in tsaro daga ɗaya daga cikin manyan hukumomin tsaro na Najeriya, wanda ake zargin babban mamba ne a cikin ƙungiyar masu safarar mutane a yankin Kudu maso Yamma.”
“Aikin da aka tsara sosai, wanda sauran matafiya a filin jirgin suka yaba da shi, ci gaba ne da sabon shirin yaki da safarar mutane da Darakta Janar ta ƙaddamar, wanda ke nufin kai farmaki ga wuraren ɗaukar mutane, wuraren safara da hanyoyin da ake bi a cikin Najeriya.”
Adekoye ya ce waɗanda aka ceto matasa ne masu shekaru tsakanin 15 zuwa 26, waɗanda aka ɗauko daga jihohin Kano, Katsina, Oyo, Ondo da Ribas, kuma suna kan hanyarsu ne ta zuwa kasashen Iraq, Sudan, Masar, Saudiyya, Bahrain da Afghanistan.
Yayin da yake ambato daga cikin waɗanda aka ceto, Adekoye ya ce ɗaya daga cikinsu ta sha alwashin ganin mahaifinta ya fuskanci hukunci saboda ƙoƙarin safararta zuwa Iraq.
Ya ƙara da cewa wata daga cikin waɗanda aka ceto ta bayyana cewa an yaudari mahaifiyarta da cewa za ta je Turai don yin aiki da samun kuɗaɗe.
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link