An haifi jariri da ‘fuska biyu’ a Bauchi

[ad_1]



Da wani lamari da ba kasafai ake samu ba, wata mata mai suna Hannatu ta haifi jariri mai fuska biyu da kai daya a babban asibitin gwamnatin jihar Bauchi da ke garin Azare.

Mahaifin jaririn, Malam Bala Sa’idu wanda yake a kauyen Magonshi, ya bayyana wa Aminiya cewa wannan haihuwar wata alama ce ta ikon Allah da ke tabbatar da cewa babu abin da Allah ba zai iya ba.

Ya ce duk da cewa lamarin ya bambanta da yadda aka saba, amma bai zo masa da mamaki ba.

A cewarsa, goyon cikin da matarsa ta yi ya dauki tsawon makonni 42, wanda ya zarce al’ada.

Ya gode wa babban likitan asibitin, Dr. Bello Idris, wanda ya gudanar da tiyatar cire jaririn ba tare da an caje su ko kwabo ba.

Hannatu, mahaifiyar jaririn, ta ce wannan haihuwa ta sha bamban da sauran haihuwarta takwas da ta yi a gida ba tare da zuwa asibiti ba.

Ta ce wannan karon an yi mata tiyata, kuma tana godiya ga Allah da ya ba ta wannan baiwa.

Ta kara da cewa tana kaunar danta kuma tana rokon Allah ya ba ta lafiya domin ta raine shi kamar sauran ’ya’yanta.

Dr. Bello Idris, babban likitan da ya jagoranci aikin, ya ce a duk tsawon aikinsa bai taba fuskantar irin wannan halitta ba.

Ya ce akan samu irin wannan yanayi a cikin mutum daya daga cikin mutum miliyan goma.

Ya ce jaririn na da kai daya, fuska biyu, idanu hudu, hanci biyu, baki biyu, kunne biyu, hannaye biyu da kafa biyu. Sai dai ya zo da yankakken baki da ake kira “bakin noma,” wanda ke hana shi shan nono.

Likitan ya kara da cewa da zarar mahaifiyar jaririn ta samu sauki daga tiyatar da aka yi mata, za a tura su zuwa babban Asibitin Koyarwa na Gwamnatin Tarayya (FUHSTA) da ke Azare domin ci gaba da kulawa da kuma gudanar da bincike kan sauran sassan jikinsa.

A karshe, Malam Bala Sa’idu ya roki gwamnatin jihar Bauchi, kungiyoyin agaji da daidaikun mutane da su taimaka masa wajen ganin an samu lafiyar jaririn, duba da karancin halin da yake ciki.

Ya ce tuni aka ce za a tura su babban asibiti, amma yana cikin damuwa kan yadda za su fuskanci lamarin saboda rashin kudi.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *