Me ya sa wasu ƙasashen Afirka ba sa goyon bayan kafa ƙasar Falasɗinu?




Yayin da ƙasashe irin su Birtaniya, Kanada da Ostareliya suka amince da kafa ƙasar Falasṭinu, ana tsammanin samun ƙarin wasu ƙasashe.

Shugaban Falasɗinu, Mahmud Abbas, ya yaba da wannan mataki tare da kira ga sauran ƙasashe su nuna irin wannan goyon baya.

Yawancin ƙasashen Afirka sun riga sun amince da Falasdɗinu tun shekarun 1980.

Shugabanni irin su Thomas Sankara da Nelson Mandela sun taɓa danganta gwagwarmayar Falasɗinawa da irin ta Afirka na neman ’yanci.

Amma har yanzu akwai ƙasashe biyu da ba su amince da kafa ƙasar Falasɗinu ba; wato Kamaru da Eritrea.

Kamaru

Kamaru tana da alaƙa mai ƙarfi da Isra’ila musamman a fannin tsaro.

Isra’ila na bai wa dakarun Kamaru horo, tana kuma taimaka mata wajen tabbatar da tsaron gwamnatin ƙasar.

Wannan ya sa Kamaru ba ta son lalata alaƙarta da Isra’ila.

Haka kuma, gwamnatin na tsoron idan ta goyi bayan kafa Falasɗinu, masu fafutukar ɓallewar yankin Ambazonia a cikin ƙasar za su samu ƙarin hujja.

Saboda haka, Kamaru kan guji bayyana ra’ayinta kan kafa ƙasar Falasɗinu.

Emritrea

Eritrea kuwa ta samo matsayarta daga tarihi.

Lokacin da Falasɗinu ta nemi goyon bayan Afirka a shekarun 1980, shugabanta Yasser Arafat ya fi kusanci da Habasha wadda ke da alaƙa da Tarayyar Soviet, ba da Eritrea ba, alhali a lokacin Eritrea na fama da yaƙin neman ’yanci daga Habasha.

Wannan ya haifar da ɓacin rai a tsakanin ’yan Eritrea.

Duk da haka, Shugaban Eritrea Isaias Afwerki ya taɓa nuna tausayawa ga Falasɗinu, har ma ya amince da matsayin Falasɗinu a Majalisar Ɗinkin Duniya a 2012.

Amma bai yadda da tsarin “ƙasashe biyu” na yarjejeniyar Oslo ba, yana ganin ba zai kawo zaman lafiya ba.

Sai dai matsin lamba na cikin gida na iya taso masa, domin kusan rabin jama’ar Eritrea Musulmai ne.

A mahangar masana, hakan zai yi kama da rashin adalci idan ƙasar da ta yi nasarar samun ’yanci ba ta goyi bayan wasu su ma su samu ’yanci ba.




Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *