An gano yarinya da aka sayar ₦3.7m a Ondo

[ad_1]



Jami’an ’yan sanda a Jihar Ondo sun kuɓutar da wata yarinya ’yar shekara huɗu da ta ɓace tare da gano wasu masu fataucin yara da ke gudanar da ayyukan su a yankunan Jihohin Ondo, Delta da Anambra.

An fara shari’ar ne a ranar 3 ga Fabrairu, 2025, lokacin da Sunday Kingsley da ke yankin Alagbaka Extension a garin Akure, ya ruwaito cewa ’yarsa Jesinta, ta ɓace ne a lokacin da take tare da mahaifiyarta Sunday Happiness.

Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar, Olusola Ayanlade ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar kuma aka sanarwa manema labarai a Akure ranar Alhamis.

Sanarwar wani ɓangare na cewa: An fara shari’ar ne a ranar 3 ga Fabrairu, 2025, lokacin da wani Sunday Kingsley na yankin Alagbaka Extension, a Akure ya ruwaito cewa ’yarsa mai shekara huɗu, Jesinta Sunday wacce ke zaune da matarsa, mai suna Sunday Happiness ta ɓace.

“An mayar da shari’ar zuwa Sashin kulawa, na hedkwatar rundunar ’yan sandan jihar domin gudanar da bincike mai zurfi, a ci gaba da gudanar da shari’ar, da gabatar da ƙarar a gaban Kotun Majistare ta Iyali, wanda ya kai ga tsare mahaifiyar yarinyar mai suna Nneka Onah tare da Sunday Happiness  a gidan gyaran hali na Ondo kafin daga bisani a ba su beli.

Ayanlade ya bayyana cewa, a ranar 9 ga watan Yuli, 2025, mai shigar da ƙara, wani Sunday Kingsley ya kai rahoto ga ’yan sanda cewa, an gano yarinyar da ta ɓace a Asaba, Jihar Delta.

Ya ce nan take, jami’an rundunar ’yan sanda suka fara aiki, inda suka yi nasarar ƙwato yarinyar tare da dawo da ita lafiya a Akure.

Sanarwar ta kuma bayyana yadda aka kame rukunin masu safarar yara:

“Haka kuma an kama wata mata mai suna Amaka Chukwuemeka mai shekara 30, wacce ta bayyana cewa ta sayi yarinyar a kan kuɗi Naira miliyan 3 da dubu 700.

“Ta kuma bayyana cewa ƙawarta mai suna Chinaza Owoh ’yar shekara 38 ce ta gabatar da ita ga wata mata mai suna Mabel Esimai mai shekara 58, wadda ta sakar mata yarinyar da sunan raino, inda ta samar da takardu na jabu a cikin shirin da suka yi.

“Wannan binciken ya sa aka ci gaba da bankaɗo, wanda ya kai ga kama Mabel Esimai, yayin da ake yi mata tambayoyi, ta bayyana cewa ta karɓi yarinyar daga wata mai suna Chioma Okechukwu ‘yar shekara 37, tare da umarnin a samo wanda zai saya.”

Kwamishinan ’yan sandan Jihar Ondo, Adebowale Lawal ya yaba wa Sashin kula da jinsi bisa nasarar gudanar da ayyukan. Ya kuma umurci rundunar da ta ci gaba da gudanar da bincike domin bankaɗo duk masu hannu da kuma gurfanar da waɗanda ake tuhuma a gaban kuliya.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *