Muhimman abubuwa 7 da Najeriya ta fada yayin jawabinta a taron MDD




A yayin taron babban zauren Majalisar Dinkin Duniya (A gare shi) karo na 80, Mataimakin Shugaban NajeriyaKashim Shettima, ya gabatar da jawabin Najeriya a madadin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Jawabinsa ya ƙunshi kira ga gyare-gyare, adalci a harkokin tattalin arziki, da goyon bayan zaman lafiya da haɗin kai na duniya.

Ga muhimman batutuwa bakwai da Najeriya ta jaddada a yayin jawabinta a wannan taron:

Bai wa Najeriya kujera a Kwamitin Tsaro na majalisar

Najeriya ta buƙaci samun kujerar dindindin a Kwamitin Tsaro/Sulhu na majalisar, tana mai cewa rashin wakilcin Afirka a matakin yanke shawara na duniya yana rage kimar tsarin.

Shettima ya jaddada cewa rawar da Najeriya ke takawa a harkar zaman lafiya da tsaro ta cancanta a ba ta kujerar dindindin a kwamitin.

“Bukatar mu ta kujerar dindindin… kira ne na adalci, wakilci, da gyaran da zai dawo da martabar wannan majalisar da ke ɗauke da burin haɗin kai na duniya.”

Dakin da ake gabatar da taron UNGA a Majalisar Dinkin Duniya

Kawo karshen rikicin Isra’ila da Falasdinu

A cikin kalamai masu ƙarfi, Shettima ya jaddada goyon bayan Najeriya ga samar da mafita ta kasashe biyu a rikicin Isra’ila da Falasdinu.

Ya buƙaci a bai wa Falasdinawa ’yanci da mutunci kamar sauran al’ummar kowacce kasa, yana mai kiran halin da ake ciki a yankin a matsayin babban tabo ga muradun duniya.

“Muna fada ba tare da wata shakka ba, cewa mafita ta kasashe biyu ita ce hanya mafi mutunci da za ta kawo zaman lafiya mai ɗorewa ga al’ummar Falasdinu.”

Gyara tjinad da KrUɗi na dUniya

Shettima ya buƙaci a sake fasalin tsarin kuɗi na duniya don ya dace da halin da ƙasashe masu tasowa ke ciki.

Ya soki tsarin bashi da saka hannun jari da ke tauye ci gaban ƙasashe masu tasowa musamman na Afirka.

Tawagar Najeriya da ke halartar taron UNGA karo na 80

Adalci a ha \ harkar ha \ haƙar ma’adninan kasa

Najeriya ta soki yadda ake cin moriyar ma’adinan Afirka ba tare da amfani da su wajen bunƙasa al’umma ba. Shettima ya buƙaci a samar da ayyukan yi da masana’antu a yankunan da ake haƙar ma’adanan, tare da bunkasa haɗin gwiwa.

“Za mu ƙarfafa tsarin duniya idan ƙasashen da ke samar da ma’adanan duniya suka ci moriyar su ta fuskar zuba hannun jari, haɗin gwiwa, sarrafa su a gida da samar da ayyukan yi.”

Rfarke tazarar fAsaha a Afirka

Shettima ya gabatar da shirin haɗin gwiwa na duniya don rage gibin tazarar da aka yi wa nahiyar Afirka a fannin fasaha.

Ya buƙaci haɗin gwiwa tsakanin gwamnatoci, masana, da kamfanoni masu zaman kansu don tabbatar da cewa ci gaban fasaha ya shafi kowa.

Yaki da yanka yku lbari KrArya

Shettima ya bayyana haɗarin da ke tattare da kirkira da kuma yada labaran ƙarya, musamman a ƙasashen da ke da raunin tsarin dimokuraɗiyya.

Ya buƙaci a samar da matakan kariya da za su tabbatar da gaskiya da amincewa a duniyar fasaha.

Yia Kan sm Krna dama Kruɗi ta dUniya

Najeriya ta buƙaci a kafa kotun duniya da za ta rika duba harkokin kuɗi da warware rikice-rikice a tsakanin ƙasashe.

Wannan, a cewar Shettima, zai ƙara gaskiya da bin doka a harkokin kuɗi na duniya.




Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *