Masu zanga-zanga sun ƙone matar tsohon Firaministan Nepal
[ad_1]
Rabi Laxmi Chitrakar, matar tsohon Firaministan Nepal, Jhalanath Khanal, ta rasu bayan masu zanga-zanga sun cinna wa gidansu da ke unguwar Dallu, Kathmandu wuta.
Majiyoyi sun ce masu zanga-zangar sun rufe ta a cikin gidan kafin daga baya suka cinna wa gidan wuta.
An kai ta Asibitin Kirtipur Burn Hospital amma ta rasu, saboda raunukan da ta samu.
Wannan lamari ya faru ne biyo bayan wata zanga-zanga da matasa suka fara a Nepal.
Masu zanga-zangar suna neman a sallami jami’an gwamnati saboda zargin cin hanci, nuna son kai, da matsalolin da suka shafi tattalin arziƙi.
Aƙalla mutum 22 ne suka rasu tun daga ranar Litinin, yayin da sama da 300 suka ji jikkata.
Ƙungiyar kara haƙƙin ɗan Adam ta Amnesty International, ta ce ’yan sandan Nepal sun yi amfani da harsasan gaske wajen tarwatsa masu zanga-zangar.
Wasu bidiyo da aka yaɗa sun nuna yadda aka dinga jefa abubuwa masu fashewa a gidajen manyan ‘yan siyasa, ciki har da tsofaffin Firaminista K.P. Sharma Oli, Sher Bahadur Deuba, da Pushpa Kamal Dahal.
An kuma kai wasu gine-ginen gwamnati hari, ciki har da babban ofishin gudanarwa da fadar shugaban ƙasa.
Sakamakon tashin hankali, Firaministan Nepal, Oli, mai shekaru 73, ya yi murabus don taimaka wa wajen samo mafita ta siyasa.
Wasu ministoci, ciki har da masu kula da harkokin ruwa, noma, da harkokin cikin gida, su ma sun yi murabus.
Al’amura sun rikice a ƙasar, yayin da hukumomi ke ƙoƙarin wanzar da doka da oda, tare da kira a kwantar da hankali da tattaunawa don kawo ƙarshen lamarin.
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link