Majalisa Ta Bai Wa Minista Sa’o’i 48 Ya Bayyana A Gabanta Kan Hatsarin Jirgin Abuja Zuwa Kaduna

[ad_1]

Kwamitin majalisar wakilai mai kula da harkokin sufurin kasa ya bayar da wa’adin sa’o’i 48 ga Ministan Sufuri, Sa’idu Alkali da ya gurfana a gabanta kan yadda jirgin kasan da ya taso daga Abuja zuwa Kaduna ya yi hatsari wanda ke ɗauke da fasinjoji 618 a kwanakin baya.

Kwamitin ya ɗau matakin ne a ranar Talata, biyo bayan gazawar da ministan ya yi na gurfana a gabanta domin amsa tambayoyi kan lamarin.

Shugaban kwamitin, Hon. Blessing Onuh wacce ta nuna rashin jin daɗinta kan rashin zuwan Alkali, ta ce ba za a amince da wannan ɗabi’a ba, “juya wa ‘yan Nijeriya baya a lokacin da suka fi bukatarsa ​​ba.”

Onuh ta ce, “Ba zai yi wu ba, mu bar ayyukanmu, da yawa daga cikinmu sun yanke hutun da suke kai, muka taho daga Legas saboda wannan zama amma Ministan ya yi watsi da kiran majalisar.

“An jefa ‘yan’uwanmu cikin hatsari, wannan ba abun wasa ba ne, don haka mun dakatar da taron kuma mun umarci Ministan ya bayyana a gaban wannan kwamitin cikin sa’o’i 48.”




Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp



[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *