An ceto ɗan ƙasar Masar da aka yi garkuwa da shi a Oyo

[ad_1]



Rundunar ’yan sandan Jihar Oyo ta sanar da ceto wani ɗan ƙasar Masar da wasu da ba a san ko su wane ba suka yi garkuwa da shi.

Kakakin rundunar, CSP Adewale Osifeso, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya raba wa manema labarai a Talatar nan a Ibadan, babban birnin jihar.

Ya ce an ceto ɗan Masar ɗin ne a ranar Talata da safe — kwana ɗaya kacal bayan sace shi — ba tare da an biya kuɗin fansa ba.

Osifeso ya ce an sace mutumin ne a yankin Alomaja, kusa da garin Idi-Ayunre, wani yanki da ke gefen birnin Ibadan.

A cewarsa, bayan samun rahoton garkuwar, sai Kwamishinan ’Yan Sanda na Jihar Oyo, CP Femi Haruna, ya bayar da umarnin gaggawa ga sashen yaki da masu garkuwa da mutane na rundunar.

Hakan ce ta sanya sashen ya haɗa gwiwa da rundunar ’yan sanda ta Jihar Ogun da kuma wasu mafarauta, inda suka shiga dazukan da ke tsakanin jihohin Oyo da Ogun domin kai farmaki.

Wakilinmu ya ruwaito cewa, an yi saar gaske yayin da cikin awa 24 kacal, jami’an suka ceto ɗan ƙasar Masar daga hannun masu garkuwar.

Kakakin ’yan sandan ya ƙara da cewa yanzu haka an kai mutumin Asibitin Rundunar ’Yan Sanda na Eleyele da ke Ibadan domin duba lafiyarsa.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *