Yadda rusau ya janyo zanga-zanga a Legas

[ad_1]



Wasu mazauna unguwar Oworonshoki da ke ƙaramar hukumar Kosofe a Jihar Legas, sun datse wani sashe na gadar Third Mainland a ranar Litinin, a wata zanga-zanga da suka gudanar don nuna adawa da rushe musu gidaje.

Datse hanyar da suka yi ya haddasa cunkoson masu ababen hawa da fasinjoji, lamarin da ya tilasta wa ’yan sanda tarar hanzarin lamarin, inda suka riƙa harba barkonon tsohuwa domin tarwatsa masu zangar-zangar.

Aminiya ta ruwaito cewa, tun a watan Yulin 2023 aka soma rusau ɗin, lamarin da ya raba wasu mazauna unguwanni kamar Oke-Eri, Odunfa Lane, Ogo-Oluwa, Precious Seed, Coker da kuma Mosafejo, da muhallansu.

A wani sabon rusau ɗin na yau Litinin da ya shafi unguwar Ojulari, gwamnati ta aike da jami’an tsaro domin tabbatar da an gudanar da aikin ba tare da fuskantar tirjiya ba da tsakar dare, inda suka fara rushe gidajen da ake zargin an gina su ba bisa ka’ida ba.

Da yake jawabi a madadin waɗanda lamarin ya shafa, jagoran masu zanga-zangar, Opeyemi Ogunlami, ya bayyana cewa rusau ɗin ya ɗaiɗaita rayuwar mutane da dama tare da durƙusar da tattalin arzikin al’ummar yankin.

Ya ce wannan rusau ɗin ba wai kawai iya gidaje ya shafa ba, har da daƙile fatan samun kyakkyawar makoma a rayuwar mazauna yankin.

Yadda aka yi zanga-zanga saboda rusau a Legas


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *