Ambaliyar Ruwa: NEMA ta ceto mata 2 da jaririya a Kaduna




Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Ƙasa (NEMA), ta ce ta samu nasarar ceto wasu mata biyu da wata jaririya da ambaliyar ruwa ta rutsa da su a Jihar Kaduna.

Shugabar hukumar, Hajiya Zubaida Umar ce, ta bayyana hakan a shafinta na Facebook.

Ta ce ambaliyar ta auku ne sakamakon ruwan sama mai yawa da aka yi a ranar Juma’a.

Ta ce sama da gidaje 160 da magidanta 500 ne ambaliyar ta shafa a unguwanni irin su Kabala Doki, Bachama, Kigo, Ramat, da Unguwar Dosa/Nasarawa/Mali.

Rahoton ya nuna cewa ruwan kogin Kaduna ne ya yi sama, ya shiga unguwanni, lamarin da ya haddasa ambaliyar.

Shugaban NEMA na Kaduna, Malam Suleiman Mohammed, ne ya jagoranci aikin ceto tare da haɗin gwiwar hukumomin agaji na jihar.

NEMA, ta ce za ta ci gaba da aiki tare da sauran hukumomin agaji domin tallafa wa waɗanda ambaliyar ta shafa.




Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *