Kwankwaso zai iya komawa APC – Abdulmumin Kofa
[ad_1]
Hon Abdulmumin Jibrin Kofa, dan Majalisar Wakilan Najeriya ya ce jagoran jam’iyyar NNPP na kasa, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso a shirye yake ya tattauna da jam’iyyar APC kan batun komawa cikinta.
Dan majalisar, wanda makusancin Kwankwason ne dai a ’yan makonnin da suka gabata sau biyu yana ganawa da Shugaban Kasa Bola Tinubu a fadarsa da ke Abuja a kan batun Kwankwason.
Kofa ya bayyana hakan ne yayin tattaunawarsa da gidan talabijin na Channels a shirinsu mai suna Siyasa a yau ranar Laraba.
Sai dai Kofa wanda ke wakiltar mazabar Kiru/Bebeji a majalisar ya ce ya ce wasu daga cikin ’yan jam’iyyar ta APC a jiharsu ta Kano ba za su so komawar tsohon Gwamnan na Kano ba.
Amma ya ce har yanzu ana ci gaba da tattaunawa a kan batun.
Ya ce, “Idan ka ce Kwankwaso zai koma APC, ko kuma za mu koma APC, hatta a cikin ita APC din a Kano, akwai mutane da yawa da ba za su so ya koma ba, watakila masu son zama Gwamna da ma wadanda ba Gwamnan suke son zama ba.
“Na yi iya kokarina wajen ganin siyasar Kano da ta Najeriya ta daidaita, amma tana da sarkakiya sosai.
“Amma kowa ya sani, tun daga farkon wannan gwamnatin, na yi ta fadi-tashin ganin mun yi aiki tare wajen kafa gwamnatin hadin kan kasa.
“In dai maganar komawa APC ce, ya sha nanata cewa kofarsa ta tattaunawa a bude take, kofofinmu a bude suke, komai zai iya faruwa,” in ji dan Majalisar.
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link