An kama masu safarar muggan makamai a Katsina
[ad_1]
’Yan sanda sun kama wasu mutane biyu da ake zargi da safarar makamai masu haɗarin gaske, tare da tarin harsasai, a wani samame a Jihar Katsina.
A farkon wannan mako ne ’yan sanda da ke sintiri suka tare wata mota ƙirar Volkswagen Golf, da asubahi, inda suka gano bindiga ƙirar GPMG da sauran makamai a cikinta a kan hanyar Ingawa zuwa Karkarku.
Kwamishinan Tsaro na Jihar Katsina, Dakta Nasir Mu’azu, ya sanar da cewa masu safarar makaman matasa ne masu shekara 12 da kuma 25, daga ƙauyen Ɓaure a Ƙaramar Hukumar Safana ta jihar.
Makaman da aka gano
Sun shiga hannun hukuma bayan da aka gano suna ɗauke da wata babbar bindigar sojoji mai haɗarin gaske, ƙirar GPMG.
Jami’an sun kuma gano harsasai guda 1,063 na bindigar AK-47 da kuma harsasai 232 na PKT a hannun matasan.
Binciken farko ya nuna cewa makaman sun fito ne daga Haɗejia, Jihar Jigawa, kuma ana nufin kai su zuwa Safana, Katsina.
Kwamishinan ya ce, “Ana bincike yana domin gano ƙarshen inda makaman za su kai, da kuma sauran abokan safarar makaman da kuma inda aka samo su.”
Matsakar tsaro a Katsina
Katsina ɗaya daga cikin jihohin Arewa maso Yammacin Najeriya da ke fama da hare-haren ’yan bindiga da ke satar mutane domin neman kudin fansa da kuma safarar makamai.
Wannan ya sa hukumomi ke ƙara shirin karfafa tsaro da kuma yin sintiri a hanyoyin shiga da fita daga jihar.
Gwamnatin jihar ta yi kira ga jama’a su ci gaba da bayar da rahoto idan sun ga wani abu da ba su fahimta ba, musamman game da motsin ’yan bindiga da masu safarar makamai a yankunan karkara.
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link