Mutum 13 sun rasu yayin tsere wa ’yan bindiga a Zamfara

[ad_1]



Aƙalla mutum 13 ne suka rasu, yayin da sama da 20 suka ɓace a Jihar Zamfara, bayan jirgin ruwan da suka hau domin tsere wa ’yan bindiga ya nutse.

Mazauna yankin da wasu jami’ai sun tabbatar da aukuwar lamarin a ranar Asabar.

Harin ya faru ne a ranar Juma’a a yankin Birnin Magaji, inda ’yan bindiga suka kai wa ƙauyuka biyu hari.

Mutane da dama ne suka tsere zuwa bakin kogi, inda suka riski jirgin ruwa guda ɗaya kacal.

Hakan ya sa aka jirgin da mutane sosai, lamarin da ya sa ya nutse a cikin ruwa.

“Babban yayana da ’ya’yan yayata biyu suna cikin waɗanda suka rasu,” in ji Shehu Mohammed, wani ma’aikacin lafiya a Birnin Magaji.

Sarkin yankin, Maidamma Dankilo, ya tabbatar da rasuwar mutum 13.

Amma ya ce an ceto mutum 22, sauran 22 kuma har yanzu ba a gan su ba.

Zamfara ta daɗe tana fama da hare-haren ’yan bindiga.

A makon da ya gabata, ’yan bindiga sun kashe mutum biyu tare da sace sama da 100 a wani hari da suka kai kimanin kilomita 150 daga Birnin Magaji.

Rahotanni sun nuna cewar Jihar Zamfara ta fuskanci hare-haren ’yan bindiga sama da 50 tsakanin Yulin 2024 zuwa Yunin 2025, inda aka sace mutane sama da 1,000.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *