An shafe wata 8 ana mulki babu mataimakin gwamna a Taraba

[ad_1]



Mataimakin Gwamnan Jihar Taraba, Alhaji Aminu Alkali, ya yi ɓatan dabo inda ya shafe tsawon watanni takwas ba tare da an gan shi ba.

Alkali, na fama da rashin lafiya tun a bara wanda hakan ya sa bai sake bayyana a bainar jama’a ba.

An fara kula da lafiyarsa a Asibitin Ƙasa da ke Abuja, daga baya aka kai shi ƙasar Masar domin ci gaba da jinya.

Gwamna Agbu Kefas, ya naɗa Emmanuel Lawson, ɗaya daga cikin mataimakansa, domin taimakawa wajen gudanar da ayyukan ofishin mataimakin gwamnan.

A wata wasiƙa da Sakataren Gwamnatin Jiha ya sanya wa hannu, an ce naɗin zai taimaka wajen tabbatar da ingantaccen shugabanci.

Sai dai wasu na ganin Lawson bai cancanci riƙe wannan ofishi ba saboda ba zaɓar shi aka yi ba.

Gwamnati ta ce yana murmurewa

Gwamnatin jihar ta bayyana cewa Alhaji Aminu Alkali na murmurewa daga ciwon shanyewar ɓarin jiki da ya shafi lafiyarsa da yanayin maganarsa.

Kwamishinan Lafiya na jihar, Bordiya Buma, ya kai masa ziyara a watan Maris kuma ya ce yana samun sauƙi.

“Muna farin ciki da samun sauƙi da yake yi kuma muna fatan zai dawo nan ba da jimawa ba.”

Sai dai har yanzu bai dawo bakin aiki ba.

Wasu rahotanni na cewa yana Abuja yana ci gaba da jinya, wasu kuma na cewa yana zaune a wani gida a unguwar Wuse.

A gefe guda kuma, ma’aikatansa sun ce ba sa ganinsa ba.

’Yan adawa na neman ba’asi

Wasu ‘yan siyasa da jama’a suna buƙatar gwamnati ta bayyana gaskiyar halin da mataimakin gwamnan jihar ke ciki.

“Mutanen Taraba suna da ‘yancin sanin inda mataimakin gwamna yake da halin da lafiyarsa ke ciki,” in ji Alhaji Hassan Jika Ardo, tsohon shugaban jam’iyyar APC a jihar.

Ya ce gwamnati ta daina wasa da hankalin jama’a a kan batun da dokar ƙasa ta bayyana a fili.

Dalilin da ya sa ba a sauke shi ba

Sashe na 189 na Kundin Tsarin Mulkin Najeriya ya bayyana cewa za a iya tsige mataimakin gwamna ne kawai idan kwamitin likitoci ya tabbatar cewa ba shi da ƙoshin lafiyar da zai iya kataɓus.

Wannan na buƙatar ƙuri’a daga kashi biyu bisa uku na majalisar zartarwa ta jihar.

Har yanzu ba a ɗauki wannan matakin ba.

Siyasa ta hana a ɗauki mataki

Wasu majiyoyi sun ce ana matsa wa gwamnan jihar lamba kan ya sauke mataimakin nasa, amma yana tsoron kada hakan ya rushe tsarin rabon madafun iko tsakanin yankunan jihar.

Sauya mataimakin gwamnan na iya janyo rikicin siyasa a jihar.

An taɓa fuskantar irin wannan rikici a Taraba

A shekarar 2012, Gwamna Danbaba Suntai, ya yi hatsarin jirgin sama kuma bai samu sauƙi ba na tsawon watanni.

Rikici ya ɓarke saboda ba a bayyana halin da yake ciki ba, kuma bai miƙa wa majalisa wasiƙar cewa ba zai iya ci gaba da aiki ba.

Wannan ya janyo rikici da rarrabuwar kawuna tsakanin masu goyon bayan gwamnan da na mataimakinsa.

Ra’ayoyin lauyoyi sun bambanta

Wasu lauyoyi sun ce lokaci ya yi da gwamnati za ta aiwatar da dokar ƙasa.

“Rashin lafiyar mataimakin gwamna ta shafi ci gaban jihar. Idan ba zai iya aiki ba, ya kamata ya sauka,” in ji lauya mai kare haƙƙin bil’adama, Malachy Ugwumadu.

Amma wani babban lauya, Richard Ahonaruogho (SAN), ya ce jihar ba ta cikin matsala dangane da rashin lafiyarsa.

“Muddin gwamna bai koka cewa ba zai iya aiki ba, babu buƙatar ɗaukar mataki,” in ji shi.

Jama’a sun fara gajiya

Yayin da aka shafe tsawon lokaci babu mataimakin gwamnan, mutane da dama a jihar suna fara nuna damuwa.

Wasu na ganin rashin bayyana gaskiya yana nuna rashin girmama masu kaɗa ƙuri’a.

Yanzu dai idanun mutane sun karkata ne kan gwamnan da majalisar dokokin jihar domin su bayyana gaskiya ko su ɗauki matakin doka.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *