A ɗora min laifin hatsarin jirgin ƙasan Kaduna zuwa Abuja — Shugaban NRC




Shugaban hukumar kula da jiragen ƙasa ta Nijeriya (NRC), Kayode Opeifa, ya ce ya ɗauki alhakin hatsarin jirgin ƙasan Abuja zuwa Kaduna da ya auku a ranar Talata.

Aminiya ta ruwaito cewa hatsarin ya auku ne da misalin ƙarfe 11 na safe bayan jirgin ya taso daga Abuja zuwa Kaduna.

Da yake zantawa da gidan talabijin na Channels a yau Laraba, Opeifa ya ce ba za su yi ƙasa a gwiwa ba wajen binciken abin da ya haddasa lamarin.

“Bayan neman gafarar ’yan Najeriya, a matsayina na shugaban hukumar, na ɗauki alhakin duk abin da ya faru,” in ji shi.

“Ba za mu ɗebe tsammanin faruwar irin wannan lamari ba, amma duk lokacin da hakan ta kasance, tana ƙara mana fahimtar wuraren da suke buƙatar mu inganta.”

Hukumar agajin gaggawa ta ƙasa (NEMA) ta tabbatar da cewa mutum bakwai suka ji rauni bayan aukuwar hatsarin waɗanda tuni sun samu kulawar gaggawa daga likitoci.

A jiyan ne dai NRC ta sanar da dakatar da sufurin jirgin ƙasan da ke jigila tsakanin Kaduna da Abuja har zuwa lokacin da za ta kammala bincike kan musabbabin faruwar lamarin.




Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *