Ababen hawa sun lalace yayin da motar CNG ta yi bindiga a Kaduna

[ad_1]



Aƙalla motoci biyu ne suka lalace a tashar motar Mando da ke Jihar Kaduna, biyo bayan bindiga da wata mota mai amfani da gas ɗin CNG ta yi.

Wani ma’aikacin tashar mai suna Abdulkadir Abdullahi, ya ce lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 4 na Asuba, lokacin da tankin motar bas ɗin ya fashe a cikin tashar.

Ya ce lamarin ya yi sanadin lalacewar motoci guda biyu, kuma an kwashe su daga wajen domin duba irin ɓarnar da aka yi.

A cewarsa: “Abin farin ciki, babu wanda ya rasa ransa ko ya ji rauni, domin babu fasinjoji a cikin motar a lokacin da abin ya faru. Sai dai bindigar ta tsoratar da mutanen da ke wajen.”

Abdullahi, ya kuma ƙaryata jita-jitar cewa bam ne ya fashe, yana mai cewa matsalar gas ce kawai ta haddasa lamarin.

Rahotanni sun nuna cewa harkoki sun koma yadda aka saba a tashar, wadda ke kusa da sansanin sojojin sama na Kaduna.

Rundunar ’yan sandan Jihar Kaduna, ta tabbatar da cewa ba bam ba ne ya tashi a tashar, illa matsala da ta shafi gas na wata mota.

A wata sanarwa da kakakin rundunar, DSP Mansir Hassan, ya fitar, ya ce lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 3 na Asuba a harabar kamfanin sufuri na Silver Luxury Travel.

Ya ce: “Ƙarar fashewar ce ta sa wasu suka ɗauka cewa bam ne. Amma bincike ya nuna cewa tankin wata mota ne ya fashe, saboda an cika shi fiye da ƙima.”

Rundunar ta ce babu wanda ya mutu ko ya ji rauni, sannan an killace wajen domin tabbatar da tsaro.

Kwamishinan ’yan sandan jihar, Muhammad Rabiu, ya ba da umarnin gudanar da bincike domin gano ainihin dalilin faruwar lamarin.

Haka kuma, rundunar ta buƙaci jama’a da su guji yaɗa jita-jita, musamman kan lamuran tsaro, domin kauce wa ruɗani.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *