Kano Pillars Ta Lallasa Bendel Insurance A Kano

[ad_1]

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Kano Pillars ta koma matsayi na 14 biyo bayan gagarumar nasarar da ta samu akan abokiyar karawarta Bendel Insurance da ci 4 da nema a wasan Mako na 33 na gasar Firimiyar Nijeriya da suka buga a filin wasa na Sani Abacha dake birnin Kano.

Pillars ta jefa ƙwallaye biyu kafin zuwa hutun rabin lokaci ta hannun Mustaphq Jibrin a minti na 23 da kuma Chidozie Okorie minti 10 tsakanin ƙwallo ta farko da ta biyu, bayan dawowa daga hutun rabin lokaci Sai Masu Gida suka ƙara ƙwallaye biyu ta hannun Muhammad Aminu da Bernard Ovoke.

  • Kano Pillars Ta Ƙare Zagayen Farko Na Gasar Firimiyar Nijeriya A Jan Layi
  • Kano Pillars Ta Fice Daga Jan Layi Bayan Doke El-Kanemi Warriors

Da wannan sakamakon ne ƙungiyar wadda ta lashe kofin sau 4 a tarihi ta koma matsayi na 14 a teburin gasar da maki 42 a wasanni 33 da ta buga, wasanni 5 kacal suka rage kafin a kammala kakar wasan ta bana, Pillars na fatan cigaba da samun nasara a sauran wasanninta domin cigaba da zama a gasar a baɗi.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *