Jami’an tsaro sun hallaka ’yan bindiga 100 a Zamfara, Gwamna Lawal ya jinjina musu
[ad_1]
Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya yaba wa jami’an tsaro bisa kashe ’yan bindiga 100 a jihar.
Gwamnatin jihar, ta ce wannan nasara na nuna ƙwazo da jarumtakar jami’an tsaro wajen kare rayukan al’umma.
A cewar Kwamishinan Yaɗa Labarai na jihar, Mahmud Dantawasa, wannan aiki babbar nasara ce a yaƙi da rashin tsaro da ’yan bindiga a jihar.
“Wannan nasara na nuna jajircewar jami’an tsaro, waɗanda ke sadaukar da rayuwarsu domin kare jama’a,” in ji shi.
Gwamnatin ta ce za ta ci gaba da bai wa jami’an tsaro dukkanin goyon bayan da suke buƙata domin samun nasara.
Ta kuma yi alƙawarin yin aiki tare da Gwamnatin Tarayya da sauran masu ruwa da tsaki a harkar tsaro.
Ta ƙara da cewa wannan nasara wani ɓangare ne na ƙoƙarin da ake yi na kawo ƙarshen ƙungiyoyin masu aikata laifi da wanzar da zaman lafiya a yankunan da abin ya shafa.
An kuma buƙaci al’ummar Zamfara su ci gaba da bai wa jami’an tsaro haɗin kai ta hanyar bayar da sahihan bayanai da kuma sanya ido a cikin al’ummominsu.
“Gwamnati ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba har sai an tabbatar da tsaro a kowane yanki na jihar,” in ji sanarwar.
Gwamnatin ta ce tana da yaƙinin cewa bisa ƙoƙari da haɗin kai, za a dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link