Tinubu ya amince da fitar da N3.3trn don gyara wutar lantarki

[ad_1]



Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya amince da fitar da zunzurutun kuɗi Naira tiriliyan 3.3, domin biyan tsofaffin basussukan da suka dabaibaye ɓangaren wutar lantarki, da nufin inganta samar da ruwa a faɗin Najeriya.

Gwamnatin Tarayya, ta bayyana cewa waɗannan basussuka sun taru ne tsawon kusan shekaru 10.

Ta ƙara da cewa biyan waɗannan basussuka zai bai wa kamfanonin samar da wutar lantarki damar gudanar da ayyukansu yadda ya kamata, tare da tabbatar da samun wuta mai ɗorewa ga ’yan kasa.

Ya zuwa yanzu, aƙalla kamfanonin samar da wuta guda 15 ne, suka amince da tsarin biyan kuɗaɗen, inda tuni gwamnati ta fara fitar da kason farko na kuɗaɗen ga kamfanonin.

Dangane da wannan gagarumin mataki, Kakakin Shugaban Kasa, Bayo Onanuga, ya bayyana cewa: “Wannan Naira tiriliyan 3.3 za a biya basussukan da ake bi ne.

“An fara tura kuɗaɗen ga kamfanonin samar da wutar, ana sa ran wuta za ta inganta ga ’yan ƙasa.”

Gwamnatin ta ƙara da cewa wannan shiri ba wai kawai zai inganta wutar lantarki ba ne, har ma zai buɗe kofofin zuba jari daga ƙasashen waje, samar da ayyukan yi, da kuma kyautata ayyukan yau da kullum a faɗin ƙasar.

Ita ma a nata ɓangaren, Mai Bai Wa Shugaban Ƙasa Shawara kan Harkokin Makamashi, Olu Arowolo-Verheijen, ta nanata cewa manufar wannan shiri ta wuce batun biyan bashi.

“Shiri ba yana nufin iya biyan basussuka kawai ba ne; an tsara shi ne domin gyara tsarin ɓangaren wutar lantarki gaba ɗaya, ta yadda ’yan Najeriya za su samu wuta mai inganci kuma ɗorewa.”

A ƙarshe, gwamnatin ta tabbatar da cewa za a ci gaba da gudanar da wasu gyare-gyare, waɗanda suka haɗa da inganta tsarin samar da mitoci da kuma tabbatar da cewa gidaje da masana’antu suna samun kulawa game da sha’anin wutar lantarki.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *