Motoci 3 Masu Amfani Da Gas (CNG) Sun Yi Bindiga A Tashar Mota A Kaduna

[ad_1]

Aƙalla motoci uku na alfarma masu amfani da iskar gas (Compressed Natural Gas (CNG), mallakar kamfanin sufuri na Silver Transport, sun ƙone ƙurmus sakamakon wata fashewa da ta auku da asubahin ranar Lahadi a tashar mota ta Kawo da ke jihar Kaduna, lamarin da ya tayar da hankalin jama’a tare da jawo damuwa kan tsaron amfani da irin wannan fasahar makamashi.

Rahotannin shaidu sun nuna cewa lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 3:00 na dare yayin da aka ajiye motocin domin shirin ɗaukar fasinjoji zuwa jihohi daban-daban da safe, inda fashewar ta auku a lokaci guda ta janyo gobara da ta ƙone motocin gaba ɗaya, duk da cewa babu wani mutum a ciki a lokacin da abin ya faru.

  • Gwamna Uba Sani Ya Tsawaita Shirin Sufurin Motocin CNG Kyauta Ga Al’ummar Jihar Kaduna
  • Gwamna Yusuf Ya Mika Motocin Bas Na CNG Guda 10 Ga Kungiyar NLC Reshen Kano

Wani manaja a ɗaya daga cikin kamfanonin sufurin da ke aiki a yankin Mando Motor Park, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya bayyana cewa motocin sabbi ne kuma suna cikin shirin fara aiki ne kafin wannan ibtila’i, yana mai godewa Allah da babu wanda ya jikkata ko ya rasa ransa, duk da girman ɓarnar da aka yi.

Sai dai ya bayyana damuwa kan amfani da motocin CNG, yana mai cewa akwai buƙatar ƙarin shiri da tsauraran matakan tsaro kafin a rungumi wannan fasaha gaba ɗaya, inda ya ce “har yanzu ba mu kai matakin da za mu iya sarrafa wannan tsarin ba yadda ya kamata,” yana mai nuni da yiwuwar matsalolin fasaha ko rashin isasshen horo.

A halin yanzu, jami’an ƴansanda da sauran hukumomin da abin ya shafa sun isa wurin domin gudanar da bincike kan musabbabin fashewar, yayin da ake sa ran sakamakon binciken zai fayyace ko matsalar ta samo asali ne daga tsarin gas ɗin ko wasu dalilai na daban, yayin da aka tabbatar da cewa babu asarar rayuka a lamarin.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *