Kwararru Sun Ankarar Da Manoma Kan Tunkarar Noman Kakar Bana
[ad_1]
Wasu kwararru a fannin aikin noma a kasar nan, sun bukaci manoman kasar, da su fara shirye-shiryen tunkarar aikin noma a kakar noma ta 2026.
Sun bayar da wannan shawara ce, musamman domin a kara habaka samar da wadataccen abinci a kasar tare da kuma samar da girbin amfanin gona mai yawan gaske.
- Tallafin Abinci Na Gaggawa Daga Sin Ya Isa Togo
- 2027: ADC Na Duba Yiwuwar Fitar Da Dan Takarar Shugaban Kasa Ta Hanyar Yarjejeniya — Kakakin Jam’iyya
Kazalika, sun kuma yi kira a gare su da su rungumi dabarun yin noma na zamani, domin kara habaka sana’ar tasu.
Kwararrun, sun yi wannan kira ne a taron da aka gudanar a cikin kasidun da suka gabatar daban-daban, domin yin nazarin shirin aikin noma na bana,
Kungiyar AGAN ce, ta shirya taron a ma’aikatar aikin noma ta Jihar Neja.
Jami’in kungiyar a jihar, wanda kuma shi ne babban shugaban kungiyar Hussaini Iliyasu, ya bayyana hakan ne a jawabinsa a wajen taron.
Mahalarta taron, sun tattauna kan dabarun da ya kamata a dauka, domin a kara habaka fannnin na aikin noma, wanda hakan zai kuma sanya, manoman kasar su samu girbi mai yawa.
Ya bayyana cewa, daya daga cikin kalubalen da moman kasar ke ci gaba da fuskanta shi ne, rashin iya zuba takin zamani a shukarsu.
Ya kara da cewa, kungiyar na kuma ci gaba da yin kokarin taimaka wa manoman, domin kauce wa wannan kalubale na rashin iya zuba takin.
A cewarsa, manoman na kawai sayo takin ne, su kuma zuba a shukarsu, ko kuma idan gwamnati ta tallafa musu da takin, sai kawai su zuba shi, ba tare da bin ka’ida ba.
“Mun kirkiro da tsarin yin gwajin kasar gona, domin a taimaka wa manoman yadda za su noma gonakinsu”.
“Muna kuma koya wa manoman yadda za su rage yin dogaro kan yin amfani da takin zamanin da ke dauke da sanadarai, inda ya kara da cewa, a yanzu, muna kai wa manoman takin gargajiya, wanda ke dauke da sanadaran da ke taimaka wa amfanin da aka shuka”.
Ya sanar da cewa, yin amfani da takin na gargajiya, ya kara habaka amfanin gona da manoman suka shuka, wanda kuma ke kara lafiyar amfanin da aka shuka.
Shi kuwa, Dakta Gana Andrew Kolo, Darakta a cibiyar gudanar da bincike kan hatsi ta kasa da ke yankin Badeggi a Jihar Neja ya sanar da cewa, saboda sauyin yanayi da ake fuskanta a duniya, cibiyar ta kirkiro da wata sabuwar kimiyya wadda nan ba da jimawa ba, za ta gabatarwa da manoman kasar, wadda za ta taimaka wa manoman girbe amfanin gona mai yawa.
Ya kara da cewa, cibiyar ta kuma samar da dabaru, kan yadda manoman kasar, za su rinka zuba takin gargajiya a shukarsu wanda hakan zai kara inganta kasar nomansu.
Kolo ya kuma shawarci manoman cewa, bisa hasashen da hukumar kula da yanayi ta kasa ta yi na samun saukar ruwan damina da wuri, ya kamata manoman kasar, su fara shirye-shiryen fara yin noma.
Ya kuma bukace su, da su tabbatar da sun samu ingantaccen Irin noma, musamman Irin Shinkafa da Waken Soya.
Ya kuma bukace su da su tabbatar da sun shuka Irin noma na gajeren zango wanda ko da a ce ruwan saman bai yi nisa ba, za su iya kauce wa fuskantar matsala.
[ad_2]
Source link