Tallafin Abinci Na Gaggawa Daga Sin Ya Isa Togo

[ad_1]

A ranar Alhamis da ta gabata ce aka isar da tallafin abinci na gaggawa daga kasar Sin zuwa kasar Togo.

A yayin bikin mika tallafin a Lome, babban birnin Togo, sakatare-janar na ma’aikatar harkokin waje da kula da hadewar Afirka da ‘yan Togo mazauna kasashen waje, Afo Salifou Ousmane, ya bayyana matukar godiya da samun tallafin na Sin mai matukar muhimmanci, a madadin gwamnatin Togo.

Ya ce a halin yanzu Togo na fuskantar kalubale da suka ki ci suka ci cinyewa a fannin karancin abinci, kuma tallafin abinci daga Sin ya taimaka kwarai wajen rage matsanantan bukatun da ke addabar mafi raunanan cikin al’umma.

Ousmane ya kara da cewa, Sin ta zama muhimmiyar abokiyar hulda bisa manyan tsare-tsare wajen taimaka wa Togo kan cimma manufofinta na ci gaba, wadanda suka hada da bunkasa ababen more rayuwa, da tallafa wa tsarin kiwon lafiya, da hadin gwiwa a fannonin tsaro da aikin gona.

An isar da kashin farko na tallafin abincin ne a rabin farko na shekarar 2025, yayin da kashi na biyu ya isa a watan Fabrairu na wannan shekarar, wanda ke nuna an kammala isar da dukkan abubuwan da aka tanada a karkashin shirin. (Mai fassara: Abdulrazaq Yahuza Jere)

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *