Gwamna Uba Sani Ya Kulla Yarjejeniyar Naira Biliyan 15  Don  Inganta Wutar Lantarki  A  Kaduna

[ad_1]

Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya jagoranci  tattaunawa a taron Taron Ƙarfafa Wutar Lantarki na Kaduna wato  (Kaduna Electric Franchise Energy Summit ) da aka gudanar a kasar  Birtaniya , inda ya ƙara kaimi wajen bunƙasa samar da wutar lantarki mai dorewa domin haɓaka tattalin arzikin jihar.

A wata sanarwa da Kwamishinan Yaɗa Labarai, na jihar Kaduna  Malam Ahmed Maiyaki, ya fitar, an bayyana taron a matsayin wani muhimmin mataki na cika manufofin gwamnan na inganta masana’antu, jawo masu zuba  hannun jari, da samar da ci gaba mai ɗorewa, inda aka jaddada cewa wutar lantarki ita ce ginshiƙin ci gaban tattalin arziki.

Maiyaki  yace babban abin da ya fi jan hankali a taron shi ne rattaba hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna (MoU) da kamfanin ASI (Engineering Limited ) domin bunƙasa gyaran ɓangaren wutar lantarki da faɗaɗa kayayyakin more rayuwa. A karkashin yarjejeniyar, Jihar Kaduna za ta zuba jarin Naira biliyan 15 domin mallakar kaso 5.54 cikin ɗari a kamfanin, wanda ke nufin samun kusan kaso 4.13 cikin ɗari a Kaduna.

Sanarwar ta ce halartar gwamnan na nuna ƙudirin gwamnatin Kaduna na ƙarfafa haɗin gwiwa da ƙasashe da kamfanoni domin faɗaɗa samar da wutar lantarki da bunkasa  ci gaba.

Sanarwa ta kara da  cewa  a yayin taron, Gwamna Uba Sani ya haɗa kai da takwarorinsa na jihohin Zamfara da Kebbi wajen inganta haɗin gwiwar yankin, tare da tattaunawa da masu zuba jari kan hanyoyin samar da makamashi masu inganci.

Gwamnan ya bayyana cewa wannan zuba jari wani mataki ne na gina makomar samar da wutar lantarki mai ƙarfi a jihar, domin tallafa wa ci gaban masana’antu da kuma inganta rayuwar al’umma baki ɗaya.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *