Tinubu ya umarci yin amfani da kyamarorin tsaro a Jos

[ad_1]



Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya bayar da umarnin girka sama da kyamarori 5,000 na fasahar AI a Jihar Filato domin inganta tsaro bayan hare-haren da suka yi sanadin mutuwar mutane a Jos.

Bola Ahmed Tinubu ya kai ziyarar birnin Jos, ranar Alhamis, biyo bayan harin da aka kai ranar Lahadi da ta gabata wanda ya yi sanadin mutuwar fiye da mutane 25.

Tinubu ya bayyana hakan ne a wani taron tattaunawa da shugabannin siyasa da na gargajiya a Jos, bayan harin a Angwan Rukuba.

Ya kuma umurci hafsoshin tsaro da su kamo waɗanda suka aikata harin, tare da jaddada cewa dole ne a gano masu laifin.

Duk da haka, shugaba Tinubu ya sanar da shirin kafa kwamitin da zai tantance asarar da waɗanda abin ya shafa suka yi domin duba yiwuwar tallafa musu, yana mai cewa ko da ba za a iya mayar da rayukan da aka rasa ba, gwamnati za ta yi iya ƙoƙarinta wajen rage musu raɗaɗi kamar yadda Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *